Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, ya kalubalanci jam’iyyar APC da ta bayyana gwamnan da yake goyon bayan masu tayar da kayar baya a arewa maso yammacin Najeriya.
Aminiya ta ruwaito cewa Gwamnan ya kalubalanci jam’iyyar APC ne a wani jawabi da ya fitar gabanin ya kilace kansa saboda yiwuwar ko ya kamu da cutar Coronavirus sakamakon tafiye-tafiye da ya yi a baya-bayan nan wanda kuma ya tabbatar ya yi cudanya da wasu manyan kasar da aka gano sun kamu da cutar.
- Yadda Buhari ya gana da Daliban Kankara a cikin hotuna
- JAMB ta ba da kyautar N375m ga Jami’o’i 5 mafi kwazo a Najeriya
Jam’iyyar APC a wani bayani da ta fitar wanda mukaddashin sakataren yada labaranta Yakini Nabena ya sanyawa hannu, ta yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike a kan wani gwamna da ba ta bayyana sunansa ba saboda yana da hannu ga yawaitar tayar da kayar baya a yankin.
Tambuwal yayin mayar da martani ya ce ba wani gwamna a kasar nan da bai yi rantsuwa a lokacin kama aiki cewa zai kare rayukka da dukiyoyin mutanen da zai jagoranta ba.
Ya ce akwai mamaki idan har akwai wani gwamnan da zai yi wasa da rantsuwar da ya yi ta hanyar kawo tarzoma a cikin al’ummar da yake jagoranta.
Gwamnan ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su gayyaci Mista Nabena don ya fadi sunan wannan gwamnan a yankin kuma ya fito da hujjojinsa domin taimakawa jami’an tsaro don gaskiya ta yi halinta.