✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya ba Sarkin Musulmi fili domin gina Jami’ar Mata Zalla

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta samar da fili domin fara gina Jami’ar Mata Zalla da…

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta samar da fili domin fara gina Jami’ar Mata Zalla da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ke son ginawa.

Jami’ar wadda ta karatun kiwon lafiya ce, sunanta Nana Asma’u, kuma Gidauniyar Sultan ce za ta ginata bayan da Sarkin Musulmi ya fara tunanin kafa jami’ar sama da shekara 10 da suka gabata.

Gwamna Tambuwal ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar littafan Malaman Daular Usmaniyya  da gwamnatinsa ta dauki nauyi bugawa.

Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Filaye da Gidaje ta Jihar ta samar da fili domin soma aikin, inda ya ce gwamnatinsa a shirye take ta bunkasa ayyukkan shugabannin yanzu da wadanda suka gabata na Daular Usmaniyya.

Gwamna Tabuwal ya ce tun kafin Turawan mulkin mallaka su zo kasar nan, Daular Usmaniyya tana da tsarin shugabancinta da ya dore har yanzu.

Tun farko, Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera wanda shi ne jagoran Gidauniyar Sarkin Musulmi ya gode wa Gwamnan a madadin Sarkin Musulmi kan yadda ya taimaka musu wajen daina yin bara kafin su samu kudin buga littattafan.

“Mun tattara littattafan Mujaddadi da kannansa da dansa, mun gano akwai wadanda jingina musu kawai aka yi da wadanda aka sanya abin da ba su suka ce ba. Da farko mun buga littattafai 98 aka fassara da Larabci da Hausa da Ingilishi, aikin da ya kwashi shekara biyar muna yinsa,” inji shi.

Ya ce aikin ya ci Naira miliyan 20, kuma an buga littafai kwafe miliyan daya da dubu  shida da hamsin.

“A kashi na biyun nan Gwamna Tambuwal ya ce ba sai mun yi yawon neman taimako ba, ya ba mu Naira miliyan 98 wato kashi 50 na fara aikin, ga shi aikin ya kammala duk da wasu jarrabawa da aka samu. An buga littattafai miliyan daya da dubu 380,” inji shi.

Ya ce littattafai ne da suka yi magana kan tsaro da shugabanci da sauran mu’amala.