Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya ba da gudunmuwar Naira miliyan daya ga iyalan sojan da ya rasa rayuwarsa yayin tabbatar da an kiyaye dokar kullen coronavirus a watannin baya.
Kofur Isma’ila Ishiaku, na Bataliya ta 26 ta Rundunar Sojin Kasa ya rasu ne a wani hatsarin mota da ya auku ranar 18 ga watan Afrilun 2020 a kan titin Bodinga zuwa Tambuwal.
- Bidiyon fyade: An tsare dan hadimin Tambuwal a kurkuku
- Bidiyon fyade: Tambuwal ya umarci a kama dan mashawarcinsa
Yayin gabatar da kudin ga matar marigayin, Kwamandan Rundunar Soji ta 8, Birgediya Moses Gara, ya bayyana mamacin a matsayin soja mai kwazo da jajircewa a kan aiki.
A cewarsa, ba a taba samun marigayin sojan ba da wani laifi yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Ya nemi iyalan mamacin su dau dangana tare da fadakar da su a kan neman aminci da sauki a wurin Mai Duka.
Birgediya Gara ya ba wa iyalan mamacin tabbacin biyan su hakkokin sojan da ya riga mu gidan gaskiya.
Uwargidan mamacin, Patient Ishiaku, ta yi godiya ga Gwamna Tambuwal a kan togamashi da kyakkyawan karamci da ya yi musu.