✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 7

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba akan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.

Tambaya Ta 17: Na ji kun ce Mala’i’ku ba su shiga gidan da yake da hoto, wane irin hoto ke nan, hoton Maigida da Iyalansa? Ina neman karin bayani.
Amsa: Annabi SAW ne ya fadi haka; cewar Mala’iku ba su shiga gidan da cikinsa akwai hoto, zane ko taswirar dukkan wani abu mai rai. Wannan ya zo a cikin ingantaccen Hadisin da aka ruwaito daga Uwar Muminai Aishah RA. Amma ba laifi akan hotunan furanni da shuke-shuke.
Tambaya Ta 18: Ina tambaya ne game da amfani da baki wajen ibadar aure: Kun ce wadansu Malamai sun ce ba haramun ba ne, sai dai in maniyyi ko maziyyi ya shiga baki sannan ya zama haram. Shin sai an hadiye ne ko kuma a baki kawai? Domin wadansu sun ce sai an hadiye ne zai zama haram; don Allah ina son karin bayani.
—Dahiru Umaru.
Amsa: Kamar yadda bayani ya gabata cewa, wani bangaren na Malamai na daukar maniyyi da dangoginshi a matsayin kazanta kawai (watau khaba’ith). Shigar maniyyi da dangoginsa cikin baki haramun ne, domin su din abubuwan kazanta ne, bakin dan Adam kuwa ba wurin sanya abubuwan kazanta ba ne, don haka ba inda shari’a ta amince da shigar abin kazanta cikin baki. Allah SWT ya haramta mana ci ko shan abubuwan kazanta a cikin Al’kur’ani Mai girma; misali, a cikin Aya ta 157 cikin Suratul A’araf:
“Kuma Shi (Allah Madaukaki) Ya haramta musu abubuwan kazanta…”
Don haka dole ma’aurata su kiyaye kar wadannan abubuwa suna shiga cikin bakunansu, har in ya zamar musu dole sai sunyi haka din; da fatan Allah Ya bada ikon kiyayewa, amin.
Tambaya Ta 19: Ina so ku gaya min yadda zan shawo kan Maigidana don ya rinka dawowa gida da wuri.
Amsa: Ga shawarwarwarin duniyar ma’aura gareki:
1. Abu farko shi ne ki yi hakuri, kuma ki kara ba kanki hakuri; ki sani kowane dan Adam yana da wasu bukatu da uzurorin da suka sha bamban da na wani dan Adam din; kuma wadanda sun riga sun rikide da dabi’unsa, ta yadda zai yi wuya ya iya rabuwa ko daina aikata su farat daya komin yadda aka so haka din. Don haka kyakykyawan hakuri, shi ne magani na farko.
2. Addu’a tana maganin dukkan matsalolin rayuwa; don haka sai ki dage da yi masa addu’a a kowane lokaci, kum musamman a lokuttan amsar addu’a: kamar cikin sujjudar Salloli da lokacin zaman tahiya kafin sallama da ranar Juma’a bayan Sallar La’asar da sauransu. Sannan ki dage wajen tsaidawa da kyautata ibadarki da yawan yin nafiloli, musamman na azumi da tsayuwar dare, in sha Allahu za ki samu biyan bukatarki.
3. Ki sani, mafi yawa daga mazaje sun fi son zaman waje akan zaman cikin gida, wannan wani abu ne da ya samo asali daga ainihin gundarin halayyar da namiji. Don haka in dai ba wani aikin ashsha ne yake sa shi dadewa a waje ba, to ki yi hakuri, ki bi shi a hankali har Allah Yasa ya rage dadewa a waje sosai.
4. Ki daina jin haushin mijinki saboda wannan dabi’a akan wannan dabi’a da yake yi da baki so, matukar kina jin haushin abin, kuma kina bayyanar masa da jin haushin, to wannan ba zai sa ya daina ba, sai dai ya kara ingiza shi ma ga aikatawa.
5. Kar ki rinka yawan damunsa da mita da korafin bai dawowa da wuri, in zai tafi ki yi masa rakiya, kina mai masa addu’ar Allah Yasa a dawo lafiya cikin sakin fuska da annashuwa. In ya dawo kuma ki tarbe shi cikin sakin fuska da annaashuwa, tare da gabatar masa da dukkan abin da kika san yana bukata a wannan lokaci.
6. Ki binciki kanki da yanayin zaman ku da shi bincike mai zurfi, watakila akwai wani abu da kike yi masa wanda yasa bai son zaman gida, kamar in kina damunsa da yawan mita da korafi, ko ba ki gyara gidan ki ko yanayin yadda gidan yake ne yasa bai son zama, duk abin da kika lura yana da nasaba da matsalar sai ki yi dukkan kokarin da ya kamata ki ga cewa wannan abin ya daina faruwa.
7. Ki duba cikin ma’ajiyarki ‘yammatacinki, ki binciko hanyoyin kayatarwa da nishadanwar da za ki rinka gabatar masa, ta yadda zai ji bai ma son fita wajen ya fi son kasancewa tare da ke.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.