Tambaya ta 11: Shin lallai ne mai haila ta canja tufafinta bayan ta yi tsarki ko ta tabbatar jini bai taba tufafin ba kuma babu najasa a jikin tufafin?
Amsa: Ba lallai ba ne sai ta canja tufafinta domin jinin haila ba ya bata jiki, shi dai jinin haila yana bata abin da ya taba ne kawai, wato idan ya taba abu to sai ya zama najasa saboda haka ne Annabi (SAW) ya umarci mata su wanke tufafinsu idan jinin haila ya taba shi kuma su yi Sallah da tufafin bayan sun wanke.
Tambaya ta 12: Shin danshin da yake fito wa mace tsarki ne ko najasa, Allah Ya saka muku da alheri!
Amsa: Abin da yake sananne dai a wajen ma’abota ilimi shi ne duk abin da yake fitowa daga hanyoyi biyu to NAJASA NE sai dai abu daya ne kawai ba najasa ba- shi ne maniyyi. Shi dai maniyyi abu mai tsarki ne in kuwa ba shi ba, to duk abin da yake fitowa ma’abocin kazanta ne yake fitowa ta hanyoyi guda biyu. To wannan danshi najasa ne kuma yana daga cikin abin da yake warware alwala kuma karin bayani a kan wannan, ya kasance duk abin da yake fito wa mace na wannan ruwa najasa ne kuma dole ne ta sake alwala. Wannan shi ne abin da aka samu bayan an yi bincike tare da sashin malamai.
Sai dai in da damuwa domin sashin mata suna kasancewa tare da wannan danshi koyaushe to abin da za ta yi shi ne ta yi mu’amala irin mu’amalar wanda yake da yoyon fitsari. Sai ta rika yin alwala a lokacin kowace Sallah, idan lokacin Sallah ya yi sai ta yi alwala ta yi Sallah.
Tambayoyi kan alwala
Tambaya ta 13: Shin yana halatta in yi alwala alhali a jikina ko fatata akwai maiko ko man shafawa?
Amsa: Eh, yana halatta gare ki ki yi alwala koda a jikinki akwai maiko ko man shafawa da sharadin wannan man bai kasance wanda zai hana ruwa shiga jikinki ba kamar (Jan farce). Idan kuma ya kasance mai kauri ne wanda zai iya hana ruwa shiga fatar jiki wato kamar (Jan farce) to ba makawa sai an cire shi kafin a yi alwala.
Tambaya ta 14: Idan mace mai ciki ta ga wani jini kafin ta haihu da kwana daya ko biyu, shin za ta bar yin Azumi da Sallah saboda wannan jini ko ba za ta bari ba?
Amsa: Idan mace mai ciki ta ga jini kafin ta haihu da kwana daya ko biyu tare da tabbacin wannan jini na biki ne, to sai ta bar yin Sallah da Azumi a dalilin wannan jini.
Idan kuma babu wata alama da ta nuna ya yi kama da na biki, wato idan ba jinin biki ba ne to wannan jinin ya zama gurbataccen jini, ba zai hana ta yin Sallah da Azumi ba.
Tambaya ta 15:- Mece ce haila?
Amsa: Haila wani jini ne da ke fita da kansa daga gaban mace wadda za ta iya daukar ciki.
Mu kwana nan
Za a iya samun Ahmad Adamu Kutubi (SP) ta 08036095723