More Podcasts
Masu iya magana kan ce, banza ba ta kai zomo kasuwa.
Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su.
’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da ƙwacen waya da fyaɗe kai har ma da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a tsakanin matasa.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya
- DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Ko yaya wannan dabara take aiki?
Wannan ne abin da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan