Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanya Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a matsayin ranar soma jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar.
- Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi
- NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi
A cewarsa, an samu sauyin ranar ne domin tabbatar da muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tnade-tanaden sauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin.
Dokta Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar – wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar.
Ya ƙara da cewa, akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin.
Dubban ɗaliban Najeriya ne ke rubuta jarrabawar JAMB a kowace shekara, domin samun damar shiga makaratun gaba da sakandire.