Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da ke yawo cewa sojoji sun hana Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa.
Labarin da ya tayar da ƙura cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa, zuwa lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai ƙasar Faransa.
Wata sanarwa da Stanley Nkwocha, hadimin shugaban ƙasa kan yada labarai, ya fitar, ta ce, babu kashin gaskiya a labarin.
Sanarwar ta kara da cewa hasali ma, masu yaɗa labarin karya sun ƙirƙirar shi ne da nufin haddasa saɓani tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin nasa.