Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga amsoshin tambayoyin masu karatu kan tsaron mutuncin uwargida. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Tambaya ta 1:
Assalamu Alaikum Duniyar Ma’aurata; na ji dadin bayaninku a kan yadda uwargida za ta tsare mutuncinta, domin ya sosa mini inda yake mini kaikayi. Don Allah ku yi bayani ga mazan aurenmu don su fahimci yadda za su rika tsare mana mutuncinmu a matsayinmu na matansu. Domin maigidana ya kasance yana alfahari da irin kyawuna da iya kwalliya, don haka ba ya so in sa hijabi, musamman idan za mu fita tare, ya fi son in sanya gyale mai kyawu, kuma mai bayyana kawa. Duk ranar da na sa hijabi da kansa zai ce in koma in cire in sanya gyale, in kuma ban yi kwalliya ba, ko ban sa kaya masu kyawu ba, sai ya ce in koma in canza. To don Allah ku fadakar da irin wadannan mazajen don su gyara.
Maman Daddy, Kano.
Amsa: Da farko dai ki sani yake wannan ’yar uwa, wajibi ne yin biyayya ga mijinki cikin abubuwan da ba su saba wa dokokin Allah SWT ba, amma idan mijinki ya yi miki umarnin aikata abin da ya ci karo da umarnin Allah SWT, to wajibi ne ki yi watsi da shi. Allah ne Ya umarci ki rufe jikinki, sannan ki boye kwalliyarki ga mazan da ba muharramanki ba, shi kuma mijinki ya zo ya ce ki bude jikinki, dole ki yi wa mijinki tawaye ki bi umarnin Allah SWT, domin umarnin Allah gare mu ba abin wasa ba ne, abu ne mai muhimmanci da ya wuce duk wani umarni da wani zai yi komai matsayi da muhimmancinsa. Ki sani kin aikata babban zunubi da wannan biyayya da kika yi ga mijinki, ki gaggauta tuba ga Allah, sannan ki fara aiki da umarnin Ubangijinki wajen rufe jikinki gaba daya da boye kwalliyarki lokacin fita waje. Magidanki kuwa ki dage da yi masa addu’ar Allah Ya ganar da shi gaskiya, kuma ki rika yi masa nasiha da ban hakuri. Kada ki bari abin ya zama sanadiyyar bullar wata matsala a tsakaninku; kada ki yi fushi da duk wata magana da zai gaya miki, kuma kada ki bari barazanarsa tasa ki daina bin umarnin Ubangijinki. Ki yi hakuri ki bi shi a hankali har Allah Ya ganar da shi kuskurensa.
Fadakarwa Ga Maigidanki: Ya kai wannan bawan Allah, Ka sani cewa daya daga cikin hakkokin matar aurenka a kan ka shi ne, shiryar da ita zuwa ga hanya madaidaciya wacce za ta kai ta aljanna da tsare ta daga dukkan ayyukan da aikata su za su iya zama sanadiyyar shigarta wuta. Kamar yadda Allah SWT Ya yi Umarni ga mu’uminai cewa su kare kansu da iyalansu daga wata wuta, wacce makamashinta sun kasance mutane da duwatsu…” (kur’an; Surah 66 Aya 6).
Haka kuma Allah Ya fada cikin Littafinsa mai tsarki cewa: “Maza masu tsayuwa ne a kan mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe, kuma saboda abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu…” Wannan Aya mai albarka na nufin kai, a matsayinka na mijinta, kai ne shugabanta; kai ne jagabanta; kai ne makiyayinta mai kula da dukkan al’amuranta, kamar yadda hakkinta ne a kan ka ciyarwa, tufartawa da samar da muhalli gare ta, to haka ma yana daga cikin hakkokinta a kan ka ka tsaya tsayin daka a gare ta don ganin cewa ta tsayar da addininta kuma ta bi umarnin Allah SWT, sai kuma Ya kasance kai ne mai yi mata umarnin ta bijire wa ayoyin Allah kuma ta ketare iyakokinSa?
Ina kishinka yake ya kai wannan dan uwa? Ba ka san cewa Manzon Allah SAW Ya ce aljanna ta haramta ga mutumin da ba ya kishin iyalinsa ba? Allah Ya ni’imtaka da mata mai kyawu ga kuma iya kwalliya, ai kamata ya yi ka daraja wannan kyauta da Allah Ya yi maka, ka adana abinka ka more ta kai kadai, musamman idan ka yi la’akari da cewa kai ka biya sadaki, sannan kai ke ciyar da ita da samar da kayan kwalliya da gyaran jiki, to ai kuwa ya dace ka mori abin ka kai kadai, amma sai ga shi kana bayar da shi kyauta ga abokanka da dukkan wani mutumin da ya kalli matarka? Ka sani: kamar yadda kyawu da iya kwalliyarta ke kayatar da kai, to haka zai kayatar da duk namijin da ya kalle ta; shin ba ka jin haushi wani ya nishadantu da matarka?
Sannan ka sani matarka ta wuce matsayin abin bagu ga abokanka da sauran jama’ar gari, a ce kamar yadda za ka yi bagu da wani agogo mai tsada, ko wasu tufafi masu tsada da kasa a jikinka, haka za ka fita kana bagu kana takama da kyau da kwalliyar matarka? Iyakar matsayinta da kimarta ke nan a gare ka?
Don haka ka yi gaggawar tuba, ka fara aikin tsare kanka da iyalinka daga zama makamashin wutar jahannama, in zurfin wayewa ce irin ta zamani ta yi maka yawa, ya kamata ka surka ta da kyakkywar wayewar sanin dokokin addininka.