Mene ne ya sa idan mutum na da matsala a hanta likitoci ke cewa kada ya ci abinci mai sinadarin protein?
Amsa: Yawancin abubuwan da kan kawo ciwon hantar da zai iya kashe ta gaba daya su ne ruwan barasa da kwayar cutar birus ta hepatitis. Wadannan su ne idan suka ci hanta ba magani sai dai dashen wata. Akwai kuma cututtukan da kan taba hantar amma daga baya ta zo ta warke kamar shan wata guba misali. A wadancan cututtuka na farko ne ake cewa a rage sinadarin gina jiki na protein. Wato ba wai ana cewa masu ciwon hanta kada su ci abinci mai protein ba ne kwata-kwata, a’a ana cewa wasunsu ne su rage, tunda da wuya a hana mutum cin wannan sinadari gaba daya, domin akwai wasu abinci masu ba da kuzari amma suna kunshe da wani dan kaso na sinadari mai gina jiki a ciki.
Abin da ya sa wasu likitocin hanta suke cewa masu ciwon hantar da ya yi tsanani su rage sinadarin shi ne cewa kusan ita hanta ita ce ta fi ba da taimako wajen tsotse sinadarin da ajiye shi a hantar da ta ce gubarsa idan akwai da rarraba shi zuwa sassan jiki, wato wannan fa duk bayan an narkar da shi a ciki da hanji ke nan. To ka ga idan hanta ba lafiya, wadannan ayyuka za su yi mata wahala, a zo sinadarin maimakon ya zamo abinci sai ya zamo guba. Kuma yin hakan ba wai yana nufin shi ne zai sa hantar ta warke ba.
Shin furfura na da alaka da wahalar rayuwa ne, ko kuwa dai yanayi ne na halitta? Domin a yanzu sai in ga furfura a kan yara ko matasa.
Daga Ashiru Gwarzo
Amsa: To kusan a iya cewa duka biyun, akwai yanayin rayuwa, akwai kuma na yanayin halitta, akwai kuma na tsufa. Masanan cututtukan fata sun ce a Turawa fararen fata furfura kan fara fitowa ne a shekara 30 zuwa sama, a mutanen Asiya kuma da bakaken fata daga 40 zuwa sama. Amma suka kara da cewa ana iya samun canji daga wannan, kamar yadda kai da sauran mutane watakila za su lura cewa a shekara talatin ma ’yan Afirka ana iya samun fitowar furfura.
A lokacin da fata ta daina samar da sinadaran da ke sa gashi duhu ne ake samun furfura, kuma masanan lafiyar fata sun tabbatar cewa yanayi da canjin abinci da wurin zama da damuwa da wasu abubuwa da dama ban da tsufa, kan iya haifar da hakan. Don haka a iya cewa wani yanayi ne na rayuwa ko na wurin zama ko na canjin abinci misali. To amma sun ce ba ciwo ba ne samun furfura a kuruciya, domin ba wata illa da za ta samu wanda ya fara furfura da wuri, don haka ba abin damuwa ba ne.
Ko akwai wani ciwo da kan kawo karkacewar fuska amma ba mutuwar barin jiki ba? Domin na ji an ce mutuwar barin jiki tana kawo karkacewar fuska, kuma na san mai karkacewar fuskar amma barin jikinsa bai shanye ba.
Daga Usman Aliyu, Kano
Amsa: Eh, kwarai kuwa akwai. Duk wani ciwo da zai taba lakar fuska tun daga fitowarta a kwakwalwa har zuwa inda ta kare a kusa da haba, zai iya kawo karkacewar fuskar daya sashin fuskar, maimakon inda abin ya faru. Wato idan matsalar a dama take za a ga fuskar hagu ce a karkace. Ban da bugun jini a kwakwalwa mai kawo mutuwar barin jiki, akwai wasu matsalolin da kan iya kawo hakan, misali shigar wasu kwayoyin cuta irinsu birus cikin kunne kusa da inda lakar ta biyo, sai dai idan mutum ya samu irin wannan zogi ma ba zai bar shi ba, sai ya nemi magani cikin hanzari.
Akwai kuma wasu matsalolin daban da kan iya kawo haka, tun daga matsalar buguwa a jikin kokon kai, inda lakar ta biyo, ko wani kari ko tsuro da zai iya fitowa a fuska ya danne ita lakar. Don haka kwarai ban da ciwon bugun jini a kwakwalwa akwai abubuwan da kan kawo karkacewar fuska. Don haka mai matsalar yana iya zuwa a tantance masa mene ne ya jawo ta.
Tsokaci a kan ranar kanjamau ta bana:
A ran Talatar nan 1 ga Disamba aka yi bikin zagayowar ranar da aka ware domin fadakarwa a kan ciwon kanjamau. Taken shirin na bana shi ne: “Mun Kusa Ganin Bayansa!” Wannan ne ke nuni a kan hobbasar da ake ta yi domin ganin an kawar da ciwon kwata-kwata daga doron duniya zuwa nan da shekara 15 masu zuwa idan Allah Ya yarda. Manyan nasarorin da aka samu zuwa yanzu game da wannan matsala su ne kusan an kawar da yada ciwon daga uwa zuwa jaririnta da bai san hawa ba, balle sauka, in dai har uwar ta je cibiyar ba da magani. Sai kuma rage mace-macen masu ciwon da aka yi daga miliyan 2 a duk shekara zuwa miliyan 1 a cikin shekara goman da suka wuce. Babban kalubale da ake fuskanta shi ne na karancin magungunan da ya kamata a fara ba duk wanda aka gano da wannan matsala.
A bana an ce a kara fadakar da jama’a a kan muhimmancin sanin hanyoyin kariya daga wannan ciwo wanda a al’umarmu gwaji kafin aure ita ce babbar hanyar kariya. Da yake kuma a yanzu kyama ta ragu sosai ga masu wannan matsala, ana kira ga duk wadanda suka dade suna jinyar da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa ko mai yawan tari ko yawan rama, ko yawan gudawa, su garzaya ko a garzaya da su cibiya mafi kusa domin gwaji da bayar da shawarwari idan ma ba a samu birbishin kwayar cutar a jikin mutum ba.