✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata (1)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya a tsakanin ma’aurata.

Tambayoyi game da addu’ar karin kauna…

Ga wasu daga cikin tambayoyin da suka zo game da wannan mas’ala:

1.    Ba gardama nake ba amma ina son in ji hujjar addu’o’in da kika ce ana yi a sujadar karshe har da ayar Al’kurani Mai girma a ciki!

2. Ina miki kyakykyawan zato amma don Allah a wane ingantaccen Hadisi ne kika samo wadannan hujjoji don a rika yi a sujadar karshe don samun kauna a tsakanin miji da mata?

3. Ina neman karin bayani game da addu’ar mallaka ba a fadi adadi ba kuma wasu kalmomin ban fahimce su ba.

Amsa: Don samun karin fahimta, zan sake kawo wannan bangare kamar yadda ya gabata:

Rashin yin addu’a

Akwai sakacin rashin yin addu’a game da soyayya a tsakanin ma’aurata. Da yawan ma’aurata sukan mance su rika rokon Allah Ya dawwamar da soyayyarsu a cikin zukatansu, ya kasance al’amura da rayuwa mai kyau da marar kyau in sun taho, sai dai su kara wa soyayyar tasu karfi ba su raunatar da ita ba.

Maganin haka shi ne sai a binciki Alkur’ani Mai girma da kyawawan sunnoni da dabi’un Manzon Allah (SAW), don a samu kyawawan addu’o’i na karin soyayya da jin dadin zamantakewa a tsakanin ma’aurata. Allah Ya tanadar mana kowane irin jin dadin rayuwar duniya cikin LittafinSa mai cike da alherai da Sunnar ManzonSa (SAW) amma sai ya kasance muna musu rikon sakainar kashi, ba ma amfani da su wajen kaucewa ko warware matsalolin rayuwarmu da zamantakewarmu.

Ga wasu daga cikin irin wadannan kyawawan addu’o’i, sai a dage a rika yi ko da a cikin sujadar karshen kowace Sallah ce, da fatan Allah Ya sa mu dace da alheran da ke cikin son Allah da bin dokokinSa, amin.

1. Rabbana! Hablana, min azwajina, wa zurriyatina, kurrata a’ayuni waj’alna lil muttakina imama.

2.    Allahumma inni as’aluka an taj’ala hubbi, fiy kalbi zauji, wa yarani kama yara jahahu fi munadirati fi kulli wakti; fi aunihi hadiran au safaran. Ya Rabbil Alamin; ajib du’a’i, wagfir liy zunubi, waj’al fi kulli amri inda zauji mashkuran fi baitihi min sairihi ma wajadtani indahu.

Addu’a ta biyu domin uwargida na kawo ta, ta rika yi cikin kowace sujadar karshen kowace Sallarta don dawwamar da soyayyarta cikin zuciyar maigida, amma maigidan da ya ji yana bukatar mallake uwargidansa, to inda aka sa zauji (mijina) sai ya sa zaujati (matata) da fatan Allah Ya amsa mana addu’o’inmu, amin.

Amsa: Ya tabbata a Hadisi ingatacce cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Mafi kusancin da bawa zai iya kaiwa ga Ubangijinsa shi ne lokacin sujuda don haka ku yawaita addu’a.” A wani kaulin kuma ya ce “Ku dage da addu’a cikin sujuda akwai yiwuwar a amsa muku.” A fahimtar wadansu daga cikin malamai mutum zai iya addu’a cikin harshensa in bai iya Larabci ba; haka mutum zai iya karanta wasu daga cikin kyawawan addu’o’in da suka zo daga Kur’ani da Sunnah. Ayar Kur’ani a nan addu’ar kadai aka gabatar ba gaba dayan ayar ba. Ga yadda cikakkiyar ayar take: “Kuma wadanda suke cewa ya Ubangijinmu! Ka ba mu sanyin idanu daga matanmu da zurriyarmu kuma Ka sanyamu shugabanni ga masu takwa.” Aya ta 74 cikin Suratul Furkan.

A fahimtata ba laifi don mutum ya roki Ubangijinsa da misalin addu’ar da Ubangijinsa Mai girma da daukaka Ya bayyanar; wato ya ce a cikin sujadarsa: “Ya Ubangijina! Ka ba ni sanyin idanu daga matana da zuriyata kuma Ka sanya ni shugaba ga masu takawa.”

Sannan addu’a ta biyu an dan samu kura-kurai a cikinta a wancan karon, ga yadda take:

Allahumma inni as’aluka an taj’ala hubbi, fiy kalbi zauji, wa yarani kama yara wajhahu fi kulli waktin; hadiran au safaran. Ya Rabbil Alamin! Ajib du’a’i, wagfir li zunubi, waj’al fi kulli amri inda zauji mashkuran fi baitihi wa haisu ma wajadtani indahu.”

Fassara: Ya Allah! Ina rokonKa da Ka sanya soyayyata a zuciyar mijina, kuma ya rika ganina kamar yadda yake ganin fuskarsa a cikin kowane kallonsa, kuma a kowane lokaci, yanzu da lokacin tafiya. Ya Ubangijin Talikai, Ka amsa addu’ata, Ka gafarta min zunubaina, kuma Ka saka cikin dukkan alamurana ga mijina abin godiya a cikin gidansa kuma a duk inda ya same ni.”

A takaice dai wannan addu’a ba wani lakani ce ba, kawai misali ne na yin addu’ar neman karin soyayya a tsakanin ma’aurata cikin harshen Larabci maimakon Hausa, lokacin sujuda saboda wancan Hadisi da ya gabata, za a iya yin su a kowane lokaci ba dole sai lokacin sujuda ba, za a iya yi lokacin saukar ruwan sama, lokacin halin tafiya, tsakanin kiran Sallah da Ikama, bayan Sallar La’asar din ranar Juma’a da sauran lokutan amsar addu’a, ba lallai sai misalin da ya zo a nan ba, na yi amfani da sujuda ne saboda ta fi zama dabi’a sama da sauran, kullum akalla mutum zai yi sujada 34 a cikin salloli biyar na farilla; sannan babu adadin ko so nawa za a yi, ba kuma dole sai wadannan addu’o’in ba; mutum na iya cewa; “ Ya Allah! Ka kyautata soyayya da fahimtar juna tsakanina da matata/mijina” Ya wadatar! Da fatan Allah Ya amsa mana kyawawan addu’o’inmu a koyaushe, amin.