✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin wutar lantarki ya lakume biliyan 135 a wata 3 —Gwamnati

Gwamnatin ta ce daga watan Afrilu zuwa Yuni kuɗin sun karu daga biliyan 36 da ake biya a baya

Gwamnatin Tarayya ta ce kudin da take kashewa wajen biyan tallafin wutar lantarki ya karu daga Naira biliyan 36 zuwa biliyan 135.2 a watanni uku na biyu na shekarar 2023.

Alkaluman na kunshe ne a cikin wani rahoto na zango-zango da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta fitar a ranar Talata.

A cewar rahoton, “An sami karin kaso 275 cikin 100, wato sama da Naira biliyan 99.21, idan aka kwatanta da Naira biliyan 36.02 din da aka biya watanni uku na farkon shekarar.

“Hakan na da alaka ne da yunkurin gwamnati na ganin ta daidaita farashin wutar lantarki domin hana shi tashin gwauron zabo.”

Rahoton ya ce aƙalla gwamnatin takan kashe Naira biliyan 45 a kowanne wata a cikin watannin na Afrilu zuwa Yuni.

Kazalika, rahoton ya ce jimillan kudaden da dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki suka tara a tsakanin lokacin shi ne biliyan 267.61, daga cikin biliyan 352.61 din da ya kamata a ce kwastomomi sun biya.

NERC ta kuma ce jimillar wutar da aka samar a lokacin ita ce gigawatt 8,867.05 a kowanne awa, wanda hakan ke nuna raguwar kaso 5.17 cikin 100 idan aka kwatanta da gigawat 9,350.24 da aka samar a farkon shekarar.

Hukumar ta ce an samu raguwar ce sakamakon matsalar da injina 16 daga cikin 26 da suke samar wa kasar lantarki suka samu.