Kwanaki biyu bayan da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga abokan hulɗarta da ke ƙarƙashin tsarin Band A, gwamnatin tarayya ta yi nuni da cewa za a ƙara irin wannan matakin ga wasu.
Da yake bayani a wani taron tattaunawa da aka yi a Abuja, ranar Juma’a, Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan wani gwaji ne na cire tallafin wutar lantarki a ƙasar.
- An dakatar da kwamishina kan abincin buɗa baki a Jigawa
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Tsarin Raba Wutar Lantarki?
Ya ce, gwamnati na shirin cire duk wani tallafin da ake bayarwa a fannin don ba da damar bunƙasar zuba jari a ɓangaren wutar lantarki.
Ministan ya kara da cewa naira 225 da aka kayyade akan kowanne kilowatt guda ga abokan huldar da ke cikin tsarin Band A ana cajin su kadan ne idan aka kwatanta da naira 500 da suke biya.
Yayin da yake bayyana cewa Najeriya na fama da matsalar game da shirin bayar da tallafi inda gwamnati ke samar da kaso mai yawa na samar da lantarki, la’akari da cewa tana tallafawa da kashi 67 na lantarki, hakan ba karamin koma baya yake haifar mata ba ga bangaren zuwa jari.