✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mata kuma ’ya’ya dan majalisar Kwara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mata kuma ’ya’ya biyu na Dan Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Lawal Ayanshola Soliu.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mata kuma ’ya’ya biyu na Dan Majalisar Dokokin Jihar Kwara mai akiltara kananan hukumomin Ipaiye/Malete/Olooru, Honorabul Lawal Ayanshola Soliu.

Zugar maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kutsa gidan Honorabul Lawal Ayanshola Soliu ne da talatainin daren Litinin, “suna harbi babu kakkautawa, suka tafi da iyalan dan majalisar,” in ji wani shugaban al’umma a yanki Shao, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Ya ce “Wani daga cikin masu garkuwar ya kira yana neman kudin fansa, amma ya ce ba ya tare da sauran abokansa da za su daddale kan yawan kudin da za a biya.”

Wakilinmu ya kira wayar Honorabul Lawal Ayanshola Soliu a ranar Talata amma babu amsa.

Amma shugaban ’yan banga na yankin, Alhaji Ibrahim Saka, ya tabbatar da sace iyalan, inda ya ce, “jami’anmu suna bin sawun bata-garin a daji domin gano inda aka kai iyalan”.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kwara Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da sace iyalan dan majalisar amma ya ce, “har yanzu ba mu da cikakken bayani”.

Karo na biyu ke nan da aka yi garkuwa da iyalan dan majalisar, wanda a watan Satumbar bara aka yi dauke matarsa da dansa, ba a sako su ba sai da aka biya kudin fansa.

A lokacin, Okasanmi ya ce an kashe biyu daga cikin masu garkuwar a yayin da suke rabon kudin fansar da aka ba su a cikin daji a Karamar Hukumar Moro ta jihar.