✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta ba Isra’ila wa’adin ficewa daga Gaza ko ta kuka da kanta

Iran ta ba wa Isra'ila nan da wasu awanni ta dakatar da barnar da take wa Falasdinawa a Zirin Gaza ko kuma ta kuka da…

Gwamnatin Iran ta ba wa Isra’ila nan da wasu awanni ta dakatar da barnar da take wa Falasdinawa a Zirin Gaza ko kuma duk abin da ya same ta, to ta kuka da kanta.

Iran ta bayyana cewa ya zama tilas ta taka wa Isra’ila burki tare da ladabtar da ita kan irin kisan kiyashin da take wa Falasdinawa a Zirin Gaza.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce nan da sa’o’i masu zuwa za ta dauki mataki kan Isra’ila, wadda ta shafe kwanaki 8 tana luguden bama-bamai a Zirin Gaza, inda ta hallaka Falasdinawa kimanin 2,000.

Ministan ma’aikatar, Hossein Amirabdollahian, ya ce cin kashin da Isra’ila ke wa Falasdinawa zai iya haifar da yaki a daukacin Gabas ta Tsakiya, don haka Isra’ila ta shiga taitayinta.

Hossein Amirabdollahian ya ce, “idan har Isra’ila ba ta dakatar da laifukan yaki da take aikatawa a kan Falasdinawa a Gaza ba, to ta jira nan da da sa’o’i ta ga abin da zai biyo baya daga mayakan hadin gwiwa.”

Iran ta yi wa wannan Isra’ila jan kunnen ne duk da gargadin da kasashen Yamma suka yi mata kan rura wutar rikicin Isra’ila da kungiyar Falasdinawa ta Hamas.

Hakan kuma na zuwa na a yayin da Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta kira taron gaggawa da za ta yi ranar Laraba kan rikicin wanda Isra’ila ta kashe kananan yara akalla 614 da kuma mata 370 a Gaza.

Mayakan hadin gwiwa na “resistance front” hadakwar kungiyoyi ne da ke samun goyon bayan Iran daga kasashen Syria da Iraki, da kuma Hezbollah ta kasar Lebanon kamar Hamas a Falasdinu.

A makon jiya Hezbollah ta gwabza fada da sojoin Isra’ila a kan iyakar Lebanon, inda ake ganin yankin zai iya zama wani sabon fagen daga tsakanin Isra’ila da Hezbollah mai dubban zaratan mayaka da kuma manyan makamai da ke iya kai hari cikin kasar Isria’ila mai zurfi.

A cikin dare ne dai wasu jiragen sojin Isra’ila suka kashe fararen hula sama da 100 a yankunan Falasdinawa na Rafa da Khan Younis da ke Kudancin Gaza.

Shirin Abinci na Duniya (WFP) ya bayyana cewa kullen da Isra’ila ta yi wa Gaza ya sa yanzu kayan abincin da ya rage a kantuna da sauran sassan yankin ba zai wuce kwana biyar ba.

Isra’ila ta bukaci Falasdinawa su fice daga Arewacin Gaza inda ta ce sojojinta za su kai kazamin samame.

Kakakin Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF), Jonathan Conricus, ya ce duk da cewa mutum sama da 600,000 sun yi kaura gabanin sojojin Isra’ila su kutsawa cikin yankin, amma har yanzu akwai dubban daruruwan Falasdinawa a Arewacin Gaza, inda ya bukace su da su yi duk abin da za su iya domin ficewa daga yankin.

A ranar Laraba Shugaban Amurka Joe Biden zai je Isra’ila inda daga nan zai tafi Jordan domin ganawa da shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas domin sasanta rikicin.