Gwamnatin Tarayya za ta bude shafin rajistar shirin tallafin N30,000 ga masu sana’o’in hannu da direbobin ababen hawa na haya daga ranar ranar 1 ga watan Oktoban 2020.
Minista a Ma’aikata Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari, Maryam Yalwaji Katagum ta sanar da haka bayanin shirin ga ‘yan jariya a Abuja.
Ta ce masu sana’o’in hannu matuka 333,000 ne za su ci gajiyar kudin karkashin shirin tallafin Kanana da Matsakaitan Sana’o’i na ‘Survival Fund’ da Gwamantin Tarayya ta bullo da shi.
Ta ce sana’o’in hannu 9,000 ne za su ci gajiyar Naira miliyan 270 da aka ware a kowace jiha a karkashin shirin.
Maryam Yalwaji ta ce a ranar 1 ga Oktoba za a fara rajistar matuka da masu sana’o’in hannu a jihohi 12 na Legas, Kano, Ribas, Bauchi, Kaduna, Filato, Borno, Ekiti, Anambra, Abia, da kuma Abuja.