✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin Korona: Trump ya rattaba hannu kan kudirin raba wa Amurkawa Dala tiriliyan 2.3

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan kudurin raba Dala tiriliyan biyu da biliyan 300 a matsayin kudaden tallafi ga Amurkawa

Daga karshe dai bayan fuskantar matsin lamba daga ’yan majalisu, Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan kudurin raba Dala tiriliyan biyu da biliyan 300 a matsayin kudaden tallafi ga miliyoyin Amurkawa domin rage radadin annobar COVID-19.

Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaban mai barin gado ya rattaba hannun ne a ranar Lahadi bayan ya wallafa labarin a shafin sa na Twitter.

Trump dai wanda yanzu haka yake hutun Kirsimetin sa a birnin Florida ya sanya hannun ne bayan fuskantar matsin lamba daga ’yan majalisun kan kudirin wanda tuni suka amince da shi a makon da ya gabata.

A baya dai, shugaban ya bukaci a kara kudaden zuwa Dala 2,000, kwatankwacin sama da Naira 900,000 ga kowanne mutum daga Dala 600 da aka tsara bayarwa tun da farko.

“Na shaida wa ’yan majalisa cewa ya kamata mu rage barnatar da kudi a gwamnatance, a kuma kara yawan kudaden da Amurkawa za su samu zuwa Dala 2,000 ga kowanne baligi, yayin da yara za su sami Dala 6,000,” inji Trump lokacin da yake sanar da sa hannu a kan kudirin.

Za a raba tallafin ne ga masu karamin karfi da kuma marasa ayyukan yi domin rage musu radadin halin-ha’ula’in da annobar COVID-19 ta jefa su a ciki.

Kafin sa hannun shugaba Trump dai, kudirin ya sami gagarumar amincewa daga dukkan mambobin jam’iyyun Democrat da Republican a zaurukan majalisun kasar biyu na Dattawa da na Wakilai