Majalisar Dattawa ta musanta zargin karbar ko sisin kobo daga Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC) a matsayin tallafin rage radadin annobar COVID-19.
Majalisar ta mayar da martani ne ga Darektan Ayyuka na Kwamitin Riko na NDDC, Cairo Ojougboh, wanda yayin hira da manema labarai ya bayyana adadin kudin da ‘yan Majalisun Tarayya suka karba.
- Hatsarin jirgi ya ritsa da mata 10 a Kebbi
- ‘Yan gudun hijirar Baga za su koma gida 26 ga watan Satumba
Dakta Cairo yayi ikirarin cewa, kowane Sanata ya karbi Naira miliyan 20 yayin da kowane Dan Majalisar Wakilai ya karbi Naira miliyan 15 a matsayin tallafin rage radadin annobar coronavirus daga NDDC.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Talata daga Kakakin Majlasar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ta musanta zargin tare da kalubalantar Ojoughboh da ya ambaci sunayen ‘yan majalisar da aka bai wa kudin.
Sanata Basiru ya ce: “Majalisar Dattawan ta fusata dsa wannan lamari da ba dauke a matsayin karami ba, kuma ta karyata cewa babu wani Sanata da ya karbi Naira miliyan 20 ko wani kudi daga NDDC a matsayin tallafin coronavirus ko wani dalili na daban.
“Majalisar Dattawan tana kalubalantar Dakta Ojougboh da ya fito karara ya bayyana hujjar zargin da ya yi ta hanyar wallafa sunayen Sanatocin da aka bai wa kudin.
“Muddin kuma ya gaza gabatar da wata hujja a kan hakan, Majalisar Dattawan na bukatar ya janye maganar cikin gaggawa sannan ya nemi afuwar jama’a”, inji sanarwar.