Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Injiniya Emmanuel Audu-Ohwavborua a matsayin sabon mukaddashin Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).
Bayanin hakan ya bulla ne ta cikin wata sanarwa da NDDC ta fitar a Yammacin ranar Alhamis.
- Amurka za ta ba mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya Dala miliyan daya
- Mun kashe ’yan Boko Haram da ISWAP 31, mun kama 70 —DHQ
Wannan dai na zuwa ne bayan da a safiyar wannan Alhamis din Shugaba Buhari ya kori Shugaban Hukumar, Mista Effiong Akwa,
“Biyo bayan amincewa da Shugaba Muhammad Buhari ya yi na korar Shugaban riko na Hukumar Raya Yankin NejaDelta daga mukaminsa, yanzu haka ya amince da mai biye masa a matsayi ya karbi ragamar gudanar da Hukumar.
“Zai ci gaba da rike matsayin ne har zuwa lokacin da za a nada wani sabon shugaban, tare da mambobin Kula da Harkokin Gudanarwar Hukumar,” a cewar sanarwar.
Kafin nada shi dai, Emmanuel ya kasance Babban Daraktan a hukumar, inda yanzu zai ci gaba da rike mukamin kafin a nada wani sabon shugaba da kuma mambobin gudanarwa na hukumar.