Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) yanzu haka na ci gaba da titsiye Daraktan Kudi na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Eno Ubi Otu.
Jami’an hukumar dai sun tsare Otu ne da misalin karfe 11:15 na safe dangane da zargin karkatar da kudaden haraji sama da Naira biliyan 25 mallakin NDDC.
- Dan siyasa ya yi karar bokansa a EFCC bayan faduwa zaben neman takara
- EFCC ta kama masu damfara ta Intanet 92 a Fatakwal
Wata majiya a Hukumar ta shaida wa Aminiya cewa, har yanzu Daraktan na tare da jami’an EFCC zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A cewar jami’an, kama Otu ya biyo bayan wani zuzzurfan bincike kan rahoton binciken kwakwaf a hukumar ta NDDC.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, amma abin ya ci tura.
Yayin da wakilin namu dai ya kira wayarsa bai amsa ba.