Hajiya Balaraba Ramat Yakubu fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa ce kuma jigo ce a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Aminiya ta gana da ita. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihin rayuwata
Da farko dai sunana Hajiya Balaraba Ramat Yakubu. An haife ni a shekarar 1958 a unguwar Kurawa a garin Kano, a nan na girma har aka sani a makarantar firamare ta Jarkasa bayan nan na samu dama na yi makarantar Ilimin manya da ke Jihohin Kano da Bauchi. Iya karatun da na yi ke nan ban yi karatu sosai ba, amma sunana ya fi na wanda ya yi karatu nisan yawo a duniyar nan.
Aiki
Ni ban taba yin aikin gwamnati ba saboda karatuna bai yi zurfi ba, amma dai na yi aikace-aikace na rubutu masu yawa.
Rubuce-Rubuce
Na fara rubuta littafan Hausa a shekarar 1987, inda daga lokacin zuwa yanzu na yi rubuce-rubuce da dama inda na rubuta littatafai irin su Budurwar Zuciya da Wane Kare ne Ba bare ba, wanda na wallafa a shekarar 1988, sai kuma Wa Zai Auri Jahila, a shekarar 1990, sai Kyakkyawar Rayuwa,a shekarar 1991 da Alhaki kwikwiyo sai wani littafina mai suna Ilimi Gishirin Rayuwa, sauran sun hada da Badariyya wanda na buga shi a shekarar 1997 da kuma Ina son sa Haka, a shekarar 2003. Har ila yau, akwai Matar Uba Jaraba da wasu da dama har da na zube wadanda ba littafai bane su, ba ya ga rubutun zube na kagaggun labarai akwai rubuce-rubucena wasan kwaikwayo wadanda hukumomi masu zaman kansu suke daukar nauyi ciki har da wasan Dare da Sannu ba ta hana zuwa ga Gata nan Gata nan ku da sauransu.
Hakazalika, na dauki wasu littafai na mayar dasu fina-finai da ma wasu labarai na fina-finan da na rubuta da ma wasu littafai dana mayar cikin harshen Turanci.
Nasara
Na samu nasara a rayuwa ta hanyar rubuce-rubuce na domin Bahaushe ya ce a san mutum a san cinikinsa domin a irin nasarar da na samu na yi suna a ciki da wajen Najeriya, duk inda na je ina jin ana yawon ba da misali da sunana ta dalilin littattafaina da ake karantawa an kuma rubuta kundin bincike a kan irin ayyukana akalla guda 80 a wasu jami’io da kwalejojin Ilimi na ciki da wajen kasar nan.
kalubale
A gaskiya kowanne aiki yana da kalubale domin na fuskanci kalubale ba dan kadan ba a wannan sha’ani namu na harkar rubutu da kuma shirya fina-finan Hausa. Ka ga misali akwai wani lokaci da na so cibiyar bincike da karatu ta Ilimi wato Kano Education Resource Centre na so su karbi littafina na So Budurwar Zuciya don amfanar dalibai sai da suka sani na buga kwafi dubu biyar, sai suka ce mini ba sa bukata wanda haka ya sa na yi asarar litattafan da ma kudina. Kasancewa ta kuma mace marubuciya sai aka fara fassara ni da cewa wannan littafi nawa na So Budurwar Zuciya abuin da ke cikinsa haka ni ma nake shi ya sa nake son in koyawa yara, sai aka fara tunkara ta da shirme ni ma sai in tunkare su da haka da kyar na ceci kai na.
Mukaman dana rike
Babu laifi na rike mukamai daidai gwargwado da suka hada da shugabar kungiyar Kallabi wacce kungiyata ce ta mata marubuta zalla wacce kuma ita ce kungiyar mata marubuta ta farko a arewa. Har ila yau, na rike mukamin ma’ajin kungiyar marubuta ta kasa reshen Jihar Kano sannan kuma na zama Mataimakiyar Shugabar kungiyar Marubuta ta Raina Kama. Bugu da kari, na zama Shugaba a Gidauniyar Murtala Muhammad, a yankin arewa na kuma zama daya daga cikin amintattu a kungiyar Arewa Film Makers da National Film Right Society of Nigeria da dai sauran mukamai da dama.
Lambobin Yabo
A gwagwarmayar rayuwa da na yi na samu kyaututtuka na lambobin yabo tun lokacin ban dade sosai da fara yin rubutu ba wajen shekarar 1999 da suka hada da Lambar Yabo ta Hukumar Ilimin Manyan da aka ba ni. An ba ni wata lamba kuma ta Rare Gem Award a kan zamantakewa da al’ada wanda WODEF ta ba ni a Abuja a shekarar 2003 na kuma samu Kambu a matsayi na biyu na a Gasar Rubutun Zube na Hausa don tunawa da Marigayi Alhaji Bashir karaye na samu lambar yabo da jinjina wanda Kwalejin Edcel da ke Kano suka ba ni da kuma wata lambar yabo ta Kwankwasiyya da aka ba ni a matsayin tsohuwar hannu a harkar rubutu.
Burina a rayuwa
Burina a rayuwa shi ne, a kullum so nake na ga iyaye sun mara wa ’ya’yansu maza da mata baya wajen yin karatu na addini da na zamani. Bana son a nuna bambanci sannan kuma ina da burin ganin na taimaka wajen kawo gyara koda da shawara ne wajen ganin an samu gyara a yanayin tarbiyyar ‘ya’yanmu musammam a wannan zamani da kullum sai addu’a saboda canjawar zamani.
Iyali
Alhamdulilahi, ina da ’ya’ya biyar (ukumaza, biyu mata). Har ila yau, ina da jikoki guda takwas.
Aikace-aikacen kungiyoyi da ziyarce-ziyarce
Ni mamba ce a wata kungiya mai suna, ANA da Raina Kama da Nilwa da Kallabi Writers, sannan na je kasashe irinsu Saudiyya da birnin Dubai da kuma Ethiopia.
Shawarata ga Iyaye Mata
Ina mai kira da babbar murya a kan iyaye su daure su sanya ’ya’yansu a makarantun boko da na addini don yanzu zamani ya canja, dole sai ka yi boko duk ilimin ka idan ba ka yi boko ba gani ake yi kai baka san me duniya take ciki ba. Yana da kyau iyaye su dukufa wajen ilimantar da ’ya’yansu mata da maza. Masu iya magana na cewa idan aka ilmantar da ‘ya mace kamar an ilmantar da duniya ne domin tarbiyyar ’ya’ya a hannun uwa take kafin dawowar mai gidan ida kuma babu tarbiyya ita za a fara dora wa laifi. Don haka iyaye ina mai kiranku da a bai wa ’ya mace dama ta samu ilimi hakan zai taimaka mana, a bangaren talla kuma ba na goyon bayan talla domin talla masifa ce ga rayuwa kuma wata masifar ma shi ne irin wannan kudin da ake samu na talla ba abin da suke karawa sai karin talauci a gida.