Ma’aikatar Ilimi karkashin gwamnatin Taliban a Afghanistan ta bayyana aniyarta ta sabunta manhaja da darussan da ake koyarwa a jami’o’in kasar.
Da yake sanar da hakan, Ministan Ilimi Mai Zurfi, Abdul Baqi Haqqani, ya ce so yake ya ga daliban da suka kamala jami’a a kasar na gogayya da takwarorinsu a ko’i’na a duniya – Amma bai fayyace abin da yake nufi da hakan ba.
- Taliban ta kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan
- Wane ne Mohammad Hasan Akhund, sabon Shugaban Afghanistan?
Ya jaddada cewa mata za su ci gaba da halartar jami’a tare da takwarorinsu maza, har zuwa matakin gaba da digirin farko.
Amma za a ware wa kowane jinsi azuzuwa, sannan wajibi ne mata su yi shiga irin ta Musulunci.
Ya bayyana hakan ne bayan ziyarar aiki da Mataimakin Fira Minista kuma Ministan Harkokin Wajen kasar Qatar, Sheikh Mohammad bin Abdur Rahman Al-Thani, ya kai birnin Kabul.
Ziyarar ta ranar Lahadi ita ce mafi girma ta farko da aka kai wa Taliban, tun bayan kafa gwamantinta na riko a Afghanistan.
– Sabuwar gwamanti ta fara aiki
Gwamantin Taliban ta daga tutartar a Fadar Shugaban Kasar Afghanistan, wanda ke alamta cewa ta fara aiki, kwanaki kadan bayan ta bayyana sunayen jami’anta.
Kaddamar da sabuwar gwamnatin a ranar Asabar, 11 ga Satumba, 2021 bayan an hambarar da gwamnatinta shekara 20 da suka gabata ya jawo surututai.
A ranar ce Amurka ta yi makokin cika shekara 20 bayan hare-haren da aka kai mata a 2001, wadanda suka lakume rayuka sama da 3,o00 da dukiyar biliyoyin daloli.
A ranar 11 ga Satumba, 2001 ne aka kai hare-haren da jiragen sama a Cibiyar Kasuwani ta Duniya da Kuma Hedikwatar Tsaron Amurka (Pentagon).
Hare-haren ne suka haifar da takaddamar da ta sa Amurka ta mamaye Afghanistan, ta kuma kwace mulki daga gwamnatin Taliban a wancan lokaci.
– Duniya ta zura ido
A halin yanzu dai – bayan janyewar dakarun Amurka da Afghanistan – duniya ta zura ido don ganin yadda kamun ludayin gwamantin Taliban na yanzu zai sha bamban da na baya.
A tsohuwar gwamnatin Taliban, mata ba su samu damar halartar makarantu ba da kuma fitowa bainar jama’a.
Amma a wannan karon, Taliban, wadda ake wa kallon mai tsattsauran ra’ayin Musulunci ta ce tsarin gwamantinta zai bambanta da na baya.
Tun a taron manema labarai da ta fara gudanar wa bayan kwace mulki, kakakin Taliban kuma mukaddashin Ministan Sadarwa a yanzu, Zabihullah Mujahid, ya yi kira ga mata da su shigo cikin gwamanti.
Ya kuma sanar da barin mata su nemi ilimi da kuma ba su duk hakkokin da Allah Ya ba su.
Bugu da kari, kungiyar ta yi alkwarin yafiya ga duk mutanen da a baya suka yake ta ko suka goyi bayan makiyanta.