Gwamnatin Taliban ta kafa sabuwar doka da ta haramta yi wa mata auren dole a kasar a Afghanistan.
Sabuwar dokar da gwamnatin ta fitar ta kuma hana tilasta wa mata yin aure, tare da yin bayani kan mallakar dukiya ga macen idan mijinta ya rasu.
- Dalilin da nake so a soke lefe da kayan daki — Fauziyya D. Sulaiman
- Rasha za ta taimaki Najeriya ta yaki ta’addanci
Sai dai kuma dokar ta umarci mata da su zauna a gida ba tare da zuwa makaranta ba, ko fitowa a shirye-shiryen gidajen talabijin a kasar.
Mutane da dama a kasar sun shiga damuwa tare da kokawa kan yadda suka ce dokokin Taliban din suke danne hakkokin matan kasar.
Tun bayan da Taliban ta karbi jagorancin kasar a watan Agusta, take fito da sabbin dokoki da suka shafi yadda mutanen kasar za su gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.