Kungiyar Taliban ta umarci kamfanonin jiragen saman Kasar Afghanistan da su dakatar da yin bulaguro da matan da basa tare da muharramansu.
A baya-bayan nan Taliban ta umarci jiragen saman Ariana Afghan hade da Kam Air haramta wa mata yin bulaguro cikin jiragensu sai dai idan suna tare da muharramansu.
- Take-taken Shugaba Buhari na ’yan PDP ne — Masani
- NAJERIYA A YAU: Yadda Maye ya cinye Aljan a Babban Taron APC
Jami’an Ma’aikatar sufurin jiragen saman Kasar sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa kungiyar ta dauki matakin ne bayan kammala tattaunawa ta musamman cikin makon da ya gabata tsakanin wakilanta da hukumar shige da fice dake birnin kabul, da kuma hukumomin jiragen saman kasar.
Daukar matakin hana jiragen saman Afghanistan yin bulaguro da mata na daga cikin matakan da suka saba wa ka’idojin al’ummar kasar, wadda sabuwar gwamnatin ke yi tun bayan kwace mulki.
Ko a makon da ya gabata kungiyar ta haramta wa maza da mata ziyartar wuraren shakatawa lokaci guda, musamman wadanda ke babban birnin kasar.
Rufe makarantun mata, hana su ayyukan gwamnati, tare da tilasta musu sauya yanayin shigarsu, ya kasance tsatsaurar akida da Taliban ta dauka wajen tafiyar da Afghanistan, lamarin da ke nuna sannu a hankali ana ci gaba da ware mata a harkokin yau da kullum.
Kazalika, jami’an ma’aikatar kula da al’umma a Afghanistan na gudanar da bincike a gaban ofisoshin gwamnati domin duba ko tsawon gemun ma’aikata ya kai wanda hukuma ta umarta, kuma suna sanya kayayyaki kamar yadda Musulunci ya bukata.
Ma’aikatar yada Kyawawan Halaye da Hana Aikata Laifuka ta gargadi ma’aikatan gwamnati cewa za su iya rasa ayyukansu idan ba su mayar da hankali kan wadannan dokokin ba.