✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban ta bukaci mata su shigo cikin gwamnatinta

Ta yi afuwa ga masu laifi tare da neman mata su shigo cikin gwamnati.

Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da yin afuwa a fadin kasar tare da kira ga mata da su shigo cikin sabuwar gwamnatinta.

Taliban ta yi hakan ne a kokarinta na kwantar da hankula a Kabul, babban birnin kasar, inda mutane suka yi ta turmitsutsi a filin jirgin sama domin ficewa daga Afghanistan bayan kungiyar ta hambarar da gwamnati kasar da Amurka ke goyon baya.

“Masarutar Musuluncin (Afghanistan) ba ta so a kuntata wa mata, muna kira da su shigo gwamnati bisa tsarin Musulunci.

“Ba a fayyace tsarin yadda gwamnati za ta kasance ba tukuna, amma kamar yadda aka saba, gwamnatin Musulunci za a yi 100 bisa 100 kuma ana bukatar kowane bangare ya shigo a dama da shi,” inji sakon da kungiyar ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar dauke da sa hannun Enullah Samangani daga Hukumar Raya Al’adu ta gwamnatin Taliban ita ce sakon farko da kungiyar ta fitar tun bayan da ta kwace gwamnati a birnin Kabul.

Sanarwar ba ta yi cikakken bayani a kan wasu batutuwa ba, amma ta ce al’ummar kasar Afghanistan Musulmi ne, sun kuma san dokokin addini da Taliban take so su kiyaye.

Ta ci gaba da cewa, “Mutanen kasar nan Musulmi ne kuma mu ba mun zo ne domin mu tursasa su shiga Musulunci ba.”

A baya dai an zargi gwamnatin Taliban da auwatar da tsauraran dokokin shari’ar Musulunci da kuma takaita mata ga zaman gida.

Sai dai a wannan karon da alama gwamnatin ta sauya kamu ludayinta, duk da cewa wasu ’yan kasar na dari-dari da ita.

Mazauna birnin Kabul na zaman jiran abin da zai iya biyo baya, tun bayan mamayar ta Taliban, wadda ta saki fursunoni ta kuma kwashe makaman tsohuwar gwamnati da Shugaban kasarta ya tsere.

A ranar Litinin, mutane sun yi dandazo a babban filin jirgin sama na birnin Kabul, suna bin wani jirgin sojin Amurka a guje a lokacin da jirgin yake tafiya, suna son barin kasar da ta koma hannun kungiyar zuwa kasar Qatar, wanda a garin hakan wasu daga cikin mutanen suka rasu.

Tuni dai jami’an tsaro da ’yan siyasa a sassan kasar suka mika iko ga Taliban a kasar wadda rukunin karshe na dakarun Amurka ke shirin ficewa daga cikinta a karshen watan Agustan da muke ciki.

%d bloggers like this: