✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Talauci zai kassara mu idan aka raba Najeriya —Osinbajo

Osinbajo ya gargadi wanda suke rajin son raba Najeriya.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce matsanancin talauci da sauran matsaloli za su addabi al’umma matukar aka bari Najeriya ta rabu.

Osinbajo ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis, yayin da ya karbi bakuncin kungiyar da ke goyon bayan tafiyar Buhari da Osinbajo (Buhari Osinbajo Dynamic Support Group).

Ya ce dukkan matsalolin tsaro da suka dabaibaye Najeriya za su zama tarihi nan da wani lokaci, kuma Najeriya za ta yi karfi ta zama babbar kasa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Laolu Akande ya fitar, Osinbajo ya ce ana bukatar hadin kan ’yan Najeriya a wannan yanayin da ake ciki.

Ya ce “Ya zama dole mu hade kanmu don cimma abin da muka sa gaba.

“Shugaban kasa ko yaushe yana jaddada burinsa na magance matsalolin kasar nan musamman harkar tsaro. Bai gaza ba, ya dukufa don ganin ya kawo mafita kan matsalar tsaro.

“Duk wanda suke son ganin kasar nan ta rabu, ko ma mene tunaninsu ya kamata mu ankarar da su a kodayaushe.

“Hadin kan wannan kasar shi ne abu mafi muhimmanci ga dukkanin bangarorinta, addinai da kowa da kowa. Ko mene tunanin mutum hadin kanmu shi ne mafi alfanu,” inji Osinbajo.

Da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar Usman Ibrahim, ya jinjinawa Mataimakin Shugaban Kasar kan yadda yake ta fadi-tashi wajen hada kan al’ummar Najeriya.