✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talata mai zuwa za a fara Gasar Zakarun Kulob na Turai

A ranar Talata mai zuwa ce ake sa ran za a fara Gasar Zakarun Kulob na Turai  ta bana. kungiyoyin kwallon kafa 32 ne suke…

A ranar Talata mai zuwa ce ake sa ran za a fara Gasar Zakarun Kulob na Turai  ta bana. kungiyoyin kwallon kafa 32 ne suke fafatawa a wannan gasa da take gudana a duk shekara.  

Masoya kwallon kafa na ganin ba ya ga gasar cin Kofin Duniya, babu wata gasa da take daukar hankali fiye da ta Zakarun Kulob ta Turai, wacce aka faro a 1956.

A gasar ce zaratan ’yan kwallo suke nuna kansu ta hanyar nuna bajinta da gogewa. Kuma gasa ce da ake yi mata lakabi da ‘in-ba- ka-yi, ba-ni -wuri.’

Kulob din Real Madrid na Sifen ne ya fi kowane kulob lashe gasar, inda ya lashe sau 13. Kuma kulob din ne ya lashe gasar a shekara uku da suka gabata a jere.  Sai kulob din AC Milan na Italiya da ya lashe sau 7 sai kulob din FC Barcelona na Sifen da kulob din Liberpool na Ingila wanda suka lashe sau biyar-biyar.

Kulob din Manchester United na Ingila ya taba lashe  kofin sau uku sai kulob din Jubentus na Italiya da ya lashe sau 1 a tarihi.

Sai dai a wannan karo masoya kwallon kafa suna ganin da wuya ne in kulob din Real Madrid zai iya sake lashe kofin ganin ya rabu da dan kwallonsa Cristiano Ronaldo wanda ya koma kulob din Jubentus na Italiya a kan Fam miliyan 100.  Sai dai kuma wadansu na ganin kulob din zai iya musamman ganin yadda yake kokari bayan da aka fara Gasar La-Liga ta Sifen ta bana, duk da rashin Ronaldo.

Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wasannin za su gudana.  Ana sa ran gidajen kallon kwallo musamman a Kudu da Arewa za su cika makil da magoya baya don ganin yadda wasannin za su kaya.