✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talata mai zuwa za a cigaba da Gasar Cin Kofin Zakarun Kulob-Kulob A Nahiyar Turai (Champions League)

A ranar Talata mai zuwa idan Allah Ya kaimu za a cigaba da buga gasar cin kofin kulob-kulob na Turai watau UEFA Champions League bayan…

A ranar Talata mai zuwa idan Allah Ya kaimu za a cigaba da buga gasar cin kofin kulob-kulob na Turai watau UEFA Champions League bayan an shafe fiye da wata biyu ana hutu.
Za a cigaba da gasar ce a matakin zagaye na biyu kamar yadda jadawalin Gasar ya nuna.
kungiyoyin kwallon kafa guda goma sha shida ne za su fafata a tsakaninsu inda ake sa ran takwas daga ciki za su haye matakin kusa da na karshe watau Kwata-Fainal.
kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus ce take rike da kofin a halin yanzu kuma tana daga cikin kungiyoyin da suka kai wannan mataki.  Idan ta samu nasarar sake lashe kofin a bana, za ta kafa sabon tarihi na kulob din da ya lashe kofin a jere.
Ana sa ran gidajen kallon kwallo da ke kasar nan za su rka cika don kashe kwarkwatar ido kamar yadda aka saba a kowane lokaci idan gasar na gudana.