✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takazza: Daga barnar ruwa zuwa zubar da jini!

Takazza da ke yankin Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa – kasancewarsa gari ne da ba sananne ba kuma wanda dalilai irin na yanayin muhalli,…

Takazza da ke yankin Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa – kasancewarsa gari ne da ba sananne ba kuma wanda dalilai irin na yanayin muhalli, gurbataccen shugabanci da rashin kyakkyawan wakilci suka boye shi daga idon duniya – wani misali ne na irin mummunan halin da al’ummomi da dama suka sami kan su ciki a Shiyyar Arewa Maso Gabas ta wannan jiha.

Bayan watanni uku kacal da farfadowar Takazza daga mummunar barnar da ambaliyar ruwa ta haddasa, a yanzu haka al’ummar wannan gari suna fuskantar barazanar tashin hankali da ta jawo zubar da jini sakamakon farmakin da wasu mahara suka kai garin inda suka rusa gidaje da dama tare da yin awon gaba da dabbobin jama’a.

Ba na jin akwai wata al’umma a wannan yanki wadda ta shiga cikin matsanancin hali irin wanda al’ummar kauyen Takazza ta sami kanta a ciki a halin yanzu ba. A hankali kaunar wanna gari sai kara shiga raina take. Sau biyu ina mu’amala da mutanen garin a cikin watan Satumba na wannan shekara.

Da farko dai mutanen garin ne suka yi tattaki zuwa gu na domin neman agaji na fatun buhuna da za su yi amfani da su wajen yin katanga ga ambaliyar ruwa da ta ke neman mamaye dan abin da ya rage daga gidajen kauyen. Domin kuwa tuni ruwan ya gama lalata dukkan amfanin gonar da suka shuka inda hatta makabartar da suka binne magabatansu a ciki sai da ruwan ya zaizaye ta kuma ya tone kaburburan.

A karo na biyu kuwa – kwanaki kadan bayan na farko – ya kasance mai cike da hadari da kasadar ban mamaki. Mutanen kauyen ne suka bukaci in kai ziyara garin don jajajantawa da yin musabaha da su. Nan take kuwa na amince da wannan bukata ta su inda a kokarin hakan na shafe kusan awa guda cikin kwale-kwale ina tafiyar kasada akan ruwa mai zurfin gaske ba tare da ina dauke da kowane irin nau’i na kariya ba (wannan wani labari ne na daban).

Wahala da zaman kunci sun zama tamkar wani bangare na rayuwarmu a wannan yanki na Arewa; saboda mun yarda sun zama jiki a garemu. Bugu da kari kuma addini da al’ada sun horas da mutanenmu kan juriya da daukar kaddara a halin tsanani da wahala. Amma duk da hakan ban san lokacin da na fara zubar da hawaye ba lokacin da wasu magidanta biyu suka nuna mini daidai wurin da ruwa ya tafi da ’ya’yansu ’yan kwanaki kadan kafin zuwa na garin lokacin ambaliyar da aka yi a farkon watan Satumba.

A dai wannan rana ce babban Limamin Takazza ya shafe awa guda cikin tsohon kwale-kwale yayin da ake kokarin tsallakar da shi zuwa gaba bayan ya kamu da matsananciyar rashin lafiya. Sai dai kuma Allah bai kadddara dawowarsa garin ba. Daidai faduwar rana labarin rasuwarsa ya iske mu a lokacin muna shirin kama hanyar komowarmu gida.

Kalilan ne daga cikin mutanen Takazza suka halarci jana’iza ko yin ban kwana da gawar limaminsu da suke matuƙar girmamawa, domin kuwa a can kan tudu aka binne shi saboda babu halin dawo da gawar gida a rufe ta.

A halin yanzu, al’amarin da ya faro daga ’yan kananan fadace-fadace a gonakin Takazza da kewaye tsakanin manoman da suke kokarin alkinta dan abin da ya rage na amfanin gonarsu bayan barnar da ambaliyar ruwa ta yi da kuma makiyaya wadanda dabbobinsu suke matukar bukatar abinci, ya fara rikidewa zuwa babban rikici. An yi kaca-kaca da gidajen jama’a tare da samun munanan raunuka inda hakan ke yin barazana ga zaman lafiya (wanda ya haddasa kwashe mata da yara daga yankin a karo na biyu cikin watanni uku) saboda mabambantan dalilai guda biyu amma masu alaka da juna.

Gamayyar abubuwa irin su talauci, karancin ilmi, tabarbarewar muhalli da sha’anin siyasar koma-baya sun tilasta wa mutanenmu yin saranda da mika wuya. Amma, Alhamdu lillahi, an fara samun matakai na wayewar kan al’umma, sanya ido da kuma shiga a dama da su cikin al’amuran al’umma.

Fatima Hajiya Gana Muhammad, haifaffiyar kauyen Takazza ce wadda kuma ta ke aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a Jihar Kaduna. Tana cike da bacin rai lokacin da muka yi magana da ita. Abin da ya bata mata rai shi ne cewa a daren jiya samari ’yan sa-kai da suka zo daga makwabtan iauyuka ne kadai (ba wai ’yan kungiyar sintiri ba) suka rika tunkarar maharan suna korar su, koda yake nan take maharan suke sake komowa su kawo wani sabon farmakin. Shi ma Hassan Takazza ransa a bace yake. Wani mai suna Mallam Wada daga kauyen Damegi, wanda ke makwabtaka da Takazza, ya shaida mini cewa ana zaman dar-dar a yankin yayin da aka girke jami’an kwantar da tarzoma da safiyar nan. Duk da haka, ya ce har yanzu a cikin firgici yake. “Muna bukatar karin jami’an tsaro,” in ji shi.

Yayin da wataƙila akwai ƙamshin gaskiya a batun da ke cewa yawan tashin hankali da ake samu a yankunan ƙananan hukumomin Guri da Kirikasamma rigingimun yanki ne da aka jima ana yin su, toh haka ma kuma fa a bayyane yake cewa yanzu rikicin ya ƙara tsanani da faɗaɗa fiye da yadda yake a baya. Ana amfani da mugayen makamai inda hakan ke ƙara yawaitar mutanen da a ke kassarawa a rikicin. Har ila yau, yanayin harkokin tsaro na ƙasa baki ɗaya da kuma sauran al’amuran da ke kawo ɓaraka za su iya haɗuwa su zamar da yankunanmu masu fadama wuraren rikici da tashin hankali, idan har muka cigaba da nuna halin ko-in-kula da nuna damuwa a fatar baki saboda kawai wasu dalilan siyasa da ba sa kan ƙa’ida.

Akwai buƙatar mu yi la’akari da yiwuwar cewa wannan rikicin da muke ganin cewa ba wani abu ba ne zai iya rikiɗewa a gabanmu muna gani (Allah ya kiyaye), ya zama wani rikici da zai haɗa da manyan ma su laifi, muggan makamai da kuma haɗin bakin shuwagabanni da ba su san aikinsu ba. A ƙasa da watanni biyu da suka wuce, an sace tare da fille kan wani soja da ke bakin aiki a cikin yanayin da yake a zahiri ta’addaci ne!

Kamar sauran garuruwan da suke yankin Fadamar Haɗeja, halin da Takazza ke ciki wani abin lura ne idan ana nazarin alkinta arzikin ƙasa. Ga shi dai Allah ya azurta yankin da wadataccen ruwa, albarkatun dazuzzuka da kuma kyakkyawar ƙasar noma wadda ba a cika samun irinta ba, don haka babban abun da ya kamata mu sanya a gaba shine cewa mu sake salo da tsarin da muke gudanar da siyasa da al’amuran mulkin mu domin su riƙa tafiya daidai da wannan arziki da AllahSWT ya yi ma na; domin gudun kar arziki ya kuma zama tsiya (kamar yadda ake gani a wasu wurare masu yawan gaske). Ba yadda za a yi mutane su yi hasarar dukkan abubuwan da suka mallaka (gonaki, dabbobi, gidaje) a ambaliyar ruwan da ake iya kare faruwarta sannan kuma a lokaci guda su kasa samun zaman lafiya gami da hasarar rayukansu a hannun mahara ‘yan ta’adda!

A zuwa gaba, ya zama wajibi mu sake yin duba da nazari kan tsarin tsaronmu na cikin al’umma don ƙarfafawa tare da ingnta shi. Mu kuma ƙarfafa dokokin da ake da su yanzu domin a iya aiwatar da su yadda ya kamata. Haka zalika, sha’anin mulki da wakilcin jama’a su kasance ana yin su bisa gaskiya, ilimi da kuma ƙwarewa.

Haƙiƙa, hanyoyin shawo kan yawaitar ambaliyar ruwa da kuma yawan faruwar al’amura na rashin tsaro wanda suke faruwa sakamakon canjin yanayi, samuwar albarkatun dazuzzuka, kyakkyawar ƙasar noma da kuma ruwa, za su buƙaci wata sabuwar al’ada ta siyasa da kuma kwarewar da za ta iya kai wa ludayin mu kan dawon tanade tanaden harkokin tsaro da kare muhalli a matakin ƙasa da ma duniya baki ɗaya.

Dr Nuruddeen Muhammad shi ne San Takarar jam’iyyar PDP na mazaɓar Sanatan Arewa Maso Gabas a Jihar Jigawa sannan tsohon Ƙaramin Minista ne a Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da kuma Ministan Watsa Labarai
08/12/2023

%d bloggers like this: