Yayin da ake ci gaba da muhawara kan zabar Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa a APC, Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce bai kamata jam’iyyar ta yi watsi da al’adar da aka saba da ita ba a Najeriya.
Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya ce ya yi amanna da salon siyasa irin na tafiya tare a matsayin yanayin da ke tabbatar da adalci a kasa.
Kalaman na shi na zuwa ne gabanin wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ya zuwa Juma’a inda ake bukatar jam’iyyun siyasa su mika sunayen ’yan takararsu Shugaban Kasa da na Mataimaka.
Ya kara da cewa yin watsi da wata sananniyar al’adar da aka saba da ita ba zai yi harkar siyasa dadi ba, kuma hakan zai haifar da wariya.
Lalong ya yi wadannan bayanan ne yayin tattaunawar shi da gidan talabijin na Trust TV ranar Laraba.
Bayanan Gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin hankula suka karkata kan Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, don zaben wanda zai yi wa Tinubu mataimaki a zaben 2023.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan cewa APC na shirin ‘yan takararta na shugabancin kasa a 2023, su kasance Musulmai baki daya.
Aminiya ta ruwaito cewa akwai tirka-tirka a Jam’iyyar APC da ma abokiyar hamayyarata PDP kan batun zaben wadanda za su zama mataimaka ga ’yan takarar nasu.
A tattaunawarsu da Trust TV, Gwamna Lalong ya ce ba yana neman zama Mataimaki ga Tinubu saboda addini ba ne.
“Ba wai saboda addina nake neman mukamin Mataimakin Shugaban Kasa ba, ina neman mukamin ne saboda na cancanta,” inji shi.
Daga nan, ya Gwamnan ya jaddada bukatar da ke akwai a tafi da kowa a tafiyar ba tare da nuna wariya ba.
Da yake jawabi dangane da irin rawar da Gwamnonin Arewa suka taka wajen kwantar da hankalin jama’a a lokacin babban zaben APC, Lalong ya ce, “A lokacin da muka zabo su (wato ’yan takarar Shugaban Kasa su biyar), ba mu yi maganar addini ba, sai dai ita siyasa na da al’adar da aka saba da ita.
“Idan jama’a suka yarda da wannan al’adar da suka saba da ita, da zarar ka hana su ita (al’adar), hakan na nufin ka maishe su saniyar ware a siyasa.”
Idan dai za a iya tunawa, tun farko, APC ta zabo Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Gwamna Kayode Fayemi na Ekit da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi hade da Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi, a kan su shiga zaben fidda gwani don fitar da dan takara daya, duk da dai tsarin nasu ya gamu da cikas.
Da yake amsa tambaya kan yadda ya tafiyar da salon siyasa na tafiya da kowa a Jiharsa, sai Lalong ya ce, “Fahimta na yi cewa, wasu rikice-rikicen da ke aukuwa a Filato, hakan na faruwa ne saboda maida wasu saniyar ware. Jama’a na ganin ba a yi da su.
“A harkar siya, masu rinjaye su ne kan gaba, su kuwa marasa rinjaye a rika ba su damar fadin albarkacin bakinsu. Muddin ka kiyaye wannan, zaman lafiya zai tabbata a yankinka,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Muna batu a kan gwamnati mai zaman lafiya alhali muna cikin matsala. Magance wannan matsalar kuwa, ba ya takaita ga cin zabe ba ne kadai, har ma da yadda za a mulki kasa.
“Yayin da ka soma tunanin haka kuwa, wajibi ne ka duba sannan ka saurari koowane bangare tare da ba shi kulawar da ta dace.”
Dangane da batun halin da gwamnonin Arewa ke ciki game da batun zaben mataimakin dan takarar jam’iyyarsu ta APC, na Filaton ya Shugaba Buhari ya bai wa gwamnonin dama a kan su zabi wanda ya fi cancanta da wannan mukamin.
A cewarsa, “Ni ma zaune nake kamar kowa ina jiran tsammani saboda wannan siyasa ce. Na ji ana ambaton sunana da na wasu nan da can.
“Dan takarar jam’iyyar shi ne shi ne a kololuwa wajen zaben mataimaki, kuma na tabbata zai yi hakan tare da hadin gwiwar Shugaban Kasa. Kodayake dai muna kyautata zaton samun hadin kai wajen zaben mataimakin, Shugaban Kasa bai ba mu umarnin zabo mataimaki ba,” inji shi.
Daga Abdullateef Salau, Baba Martins (Abuja), Abdullateef Aliyu (Legas) da Bashir Isah