✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Lawan da Akpabio ta tada kura a APC

Kotu na iya cin tarar APC kan haka.

A makon jiya ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da sunayen ’yan takarar sanatoci da Jam’iyyar APC ta tura mata kuma ciki akwai sunan Sanata Ahmad Lawan da Sanata Goodswill Akpabio.

Aminiya ta ruwaito wanda ya lashe zaben fid-da-gwani na Sanatan Yobe ta Arewa, Alhaji Bashir Machina yana cewa ba zai janye takararsa ba, domin a cewarsa shi ya lashe zaben fidda-gwanin, don haka bai ga dalilin da zai janye wa Sanata Ahmad Lawan ba.

Haka shi ma Sanata Goodswill Akpabio, an yi ta gumurzu kan takararsa.

A zaben da aka yi a ranar 27 ga Mayun bana, tsohon Mataimakin Sufeno Janar na ’Yan sanda, Udom Ekpoudom ne ya lashe zaben da aka yi a harabar firamare ta Ikot Ekpene.

Sai dai bayan zaben fid-dagwani na Shugaban Kasa, an sake yin wani zabe na daban, inda Akpabio ya samu nasara.

Sai dai Ekpoudom ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya ce zaben farko da ya samu nasara ne na gaskiya.

Su biyun Sanata Lawan da Akpabio sun yi takarar Shugaban Kasa ne a Jam’iyyar APC, inda Lawan ya sha kaye a hannun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yayin da Akpabio ya janye masa a ranar zaben.

A al’ada, ’yan takara kan sayi fom biyu, in dama ta ki, sai a koma hagu, amma sai nasu ya zo da tangarda.

Ganin sunansu a cikin ’yan takarar ya sa wadansu ke ganin an yi karfa-karfa ne wajen sa sunansu tare da yin gefe da wadanda suka lashe zaben na farko.

Son zuciya ne ba su tikiti —Dokta Dukawa

Dokta Sa’id Ahmad Dukawa, malami a Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano ya shaida wa Aminiya cewa babu wani dalili da zai sa a ba wani mutum takara ba tare da ya shiga cikin masu zawarcin kujerar a yi zaben fitar da gwani da shi ba illa son zuciya irin na siyasa.

“Kowa ya san yadda tsarin dimokuradiyya yake. Dole ne duk mai son kujera ya shiga a fafata neman kujerar da shi, amma aka tsallake hakan a kan wasu mutane.

Misali na kurkusa shi ne Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan da Sanata Godswill Akpabio wadanda kowa ya san ba su shiga an yi zaben fid-da-gwani da su ba lokacin suna can suna neman wasu kujeru na daban, amma sai ga shi jam’iyyarsu ta APC tana kokarin ba su tikitin takara. Wanan abu ne na son zuciya da son rai,” inji shi.

Ya ce kalubalen da za su iya fuskanta shi ne shari’a ta kwace tikitin “Idan wadanda aka yi wa karfa-karfa suka je kotu to ba mamaki kotu ta ce an yi musu ba daidai ba, dole a dawo musu da takararsu.

“Idan kuma ba su kai kotu ba to za su zauna a cikin jam’iyyar tare da yi mata zagon kasa,” inji shi.

Wani kalubalen da za su iya fuskanta inji Dokta Dukawa shi ne yadda abin zai shafi mutuncinsu a siyasance.

Kotu na iya cin tarar APC kan haka—Barista Mainasara Kogo

Da yake sharhi kan lamarin, masanin shari’a da huldar diflomasiyyar kasa-da-kasa Barista Mainasara Kogo Umar, ya zargi Jam’iyyar APC da yi wa dokar kasa karan-tsaye ta hanyar kakaba ’yan takara.

Barista Mainasara Kogo wanda ya kafa hujja da sasssa na 29 da na 33 da 32 da 31 da 34 da kuma 221 zuwa na 208 na dokar zabe, ya ce mika sunayensu da jam’iyyar ta yi ga hukumar zabe a matsayin ’yan takararta ya saba wa daukacin hanyoyi uku da doka ta bayar: Zaben dan takara da wakilai wato dalaget na jam’iyya ke yi, ko na mambobinta da aka fi sani da kato-bayan-kato, sai zaben dan takara ta hanyar fahimtar juna da jagororin jam’iyya ke iya yi.

“Sai dai ka ga irin haka duk bai samu ba, kasancewar ba su halarci zaben fid-da-gwanin ba, sai dai takarar neman Shugaban Kasa, bayan sun rasa wancan din ne, sai suka dawo suna neman tsayawa Sanata, alhali an riga an yi shi tare da mika sunayen wadanda suka yi nasara ga hukumar zabe gabanin kurewar ranar wa’adi da ta bayar.

Haka kuma sun gaza cika ka’idar duk wata dama da doka ta bayar na maye gurbin wadanda suka ci zaben.

“Wanda ya hada da mutuwar dan takara na ainihi, ko shi dan takarar ya sanar da cewa ya janye tsayawa takara a rubuce daga yanzu zuwa kwana 90 kafin ranar da za a yi zaben gama- gari da sauran jam’iyyu.

“A nan jam’iyyarsu na da damar sake gudanar da wani sabon zaben cikin kwana 14 bayan takardar sanarwar, sai dai a tsakanin wadanda suka fafata a yayin zaben baya kadai, ba tare da shigo da wasu sababbin ’yan takara ba.

“Ka ga ke nan koda za a sake yin wani zabe, ba dama Sanata Ahmad Lawal ko Sanata Akpabio ko Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato, ko Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da suke neman kujerar Gwamna da makamantarsu, kasancewar ba a fafata da su ba, a lokacin zaben farko da aka yi,” inji shi.

Masanin shari’ar ya shawarci wadanda suke da korafi a kan lamarin, irin su Alhaji Bashir Machina da wani daga Jihar Kebbi da ke korafi kan Sanata Adamu Aliero su je kotu su nemi hakkinsu.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen tsabtace tsarin dimokuradiyya a kasar nan.

Barista Mainasar Kogo ya ce Jam’iyyar APC na iya fuskantar tarar Naira miliyan goma kan matakin da ta dauka wanda ya bayyana a matsayin kakaba dan takara da kuma yi wa doka karan-tsaye.

Ya ce ita kanta hukumar zabe za ta kasance mai laifi da hukuncin ladabtarwa zai hau kanta kan dogaronta da cewa hurumin jam’iyya ne mika dan takara da zai wakilce ta, alhali ta yi fatali da karfin iko da doka ta ba ta cewa duk wani zabe na cikin gida dole ne ya samu wakilcinta, kafin ya zama sahihi.

Ahmed Lawan ya fafata a zaben fid-da-gwani na Sanatan Yobe —APC

Sai dai da yake jawabi game da batun, Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya shiga zaben fitar-da-gwani na neman takarar Sanata a Yobe ta Arewa da jam’iyyar ta gudanar.

BBC ta kalato daga rahoton jaridar The Nation cewa ya yi wannan kalami ne a lokacin da ya jagoranci wasu ’ya’yan jam’iyyar zuwa Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, don gabatar da zabaabben Gwamnan Jihar Ekiti Mista Biodun Oyebanji.