Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na shirin kwashe muhimman kayan zaben da ta ajiye a Babban Bankin Najeriya (CBN) bayan gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya fito takarar shugaban kasa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood ne ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis, lokacin da yake magana kan shigar siyasar da gwamnan bankin, alhali bankin ne ke da alhakin ajiye muhimman kayan zabe.
- 2023: Can ta matse wa ’yan Najeriya, dadina nake ji —Emefiele
- Naira ta fadi warwas, ’yan sisaya na neman ta ido rufe
“Tuni muka fara tuntuba tare da neman wasu wurare da za mu yi amfani da su wajen adana muhimman kayanmu (na zabe).
“Mun ma riga mun fara tattauanwa, domin muna sane da abin da halin da ake ciki, duk da cewa zaben saura wata tara.
“Ina ba ku tabbacin cewa za mu shawo kan lamarin kafin lokacin, kuma ina tabbatar muku cewa ba za mu kawo kowane irin cikas ko rudani ga zaben ba,” inji shi.
Game da kiraye-kirayen da ake wa INEC ce ta taka wa jam’iyyu burki kan tsawwala farashin fom din takara, Farfesa Mahmood ya ce hukumarsa ba ta hurumin yin hakan.
Sai dai ya ce za su yi aiki da Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), wajen sanda ido kan kudaden da jam’iyyu suke kashewa a lokacin zabe.
Ya kara da cewa za su yi aiki da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron ’yan jarida da kuma ba su damar shiga wuraren da ake gudanar da zabe a kowane lokacin zabe.
Shugaban na INEC ya kuma bayyana cewa hukumar za ta yi amfani da na’ura da kuma takardu wajen tura sakamakon zabukan 2023.
Ya bayyana cewa za a yi amfani da na’ura wajen tura zabe ne kawai a lokacin da aka samu takadda a wurin tattara sakamako.
Ya ce: “Yawancin ’yan Najeriya ba su fahimci bambancin da ke tsakanin jefe kuri’a ta intanet da kuma tura sakamakon zabe ta na’ura ba.