Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, ta gaza tabbatar da zargin wulaƙanta takardar Naira da take yi wa fitacciyar ’yar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya.
A bayan nan ne EFCC ta gurfanar da Murja a gaban kotu kan zargin cewa ta ci karo da wani bidiyonta tana tiƙar rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400.
- ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
- Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC
A ƙunshin ƙarar da ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano tun a watan Maris, EFCC ta ce laifin da take tuhumar Murja tanadi ne na Kundin Dokokin Babban Bankin Nijeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.
EFCC ta ce jami’anta sun binciki bidiyon wanda ya nuna ’yar TikTok ɗin tana tiƙar rawa gami da liƙi da takardun kuɗi ’yan Naira 500 da 1000 wanda jimillarsu ta kai Naira dubu 400 a otel ɗin Tahir da ke Kano.
A yayin zaman kotun na ranar Talatar nan, lauyar EFCC, Lily Jacobs ta gabatar da bidiyon a matsayin shaida tana mai roƙon kotun da ta yanke hukunci daidai da abin da Murjar ta aikata.
Sai dai bisa dogaro da sassa na 274 da 356 na kundin tsarin shari’ar laifuka alƙalin kotun, Simon Amobeda, ya nemi EFCC ta gabatar da wannan kuɗin na Naira dubu 400 a matsayin shaida amma ta gaza ta kuma buƙaci a ba ta lokaci.
Alƙalin ya bayyana cewa akwai nauyin da rataya a wuyansa na bai wa kowane bangare kariya tsakanin masu ƙara da wanda ake tuhuma, inda ya bayyana cewa shaidar da EFCC ta gabatar ba ta zama cikakkiya ba.
A ƙarshen alƙalin ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 13 ga watan Mayu, inda ya nanata cewa Murja ta cika ƙa’idar beli ya kuma ba da umarnin ta ci gaba da zama a hannun lauyanta, Abubakar Saka da sharaɗin zai gabatar da ita a zaman kotun na gaba.