A ranar Litinin din nan ake sa ran Jagoran Jam’iyyar APC kuma dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed, zai bayyana gaban kwamitin tantancewa ’yan takara don a tantance shi.
Majiya ta kusa da dan takarar ta ce tuni kwamitin ya tuntubi Tinubu dangane da batun tantancewar.
- Gidauniyar Daily Trust Ta Horas da ’Yan Jarida Kan Binciken Kwakwaf
- Mazauna karkara sun roki El-Rufai kada ya raba su da mastugunnansu
A cewar majiyar, “Karfe 4 na rana kwamitin ya tsayar don tantance Tinubu.”
Bayanan da APC ta fitar sun nuna baki daya, ’yan takarar shugaban kasa 23 ne kwamitin zai tantance, inda za a soma tantace 11 a ranar Litinin, ragowar 12 kuma zuwa ranar Talata.
Ga jerin sunayen ’yan takara da ake sa ran kwamitin zai tantance kamar haka:
- Chukwuemeja Uwaezuoke Nwajiuba
- Badaru Abubakar
- Robert A. Boroffice
- Uju Ken-Ohanenye
- Nicholas Felix
- Nweze David Umahi
- Ken Nnamani
- Gbolahan B. Bakare
- Ibikunle Amosun
- Ahmed B. Tinubu
- Ahmad Rufai Sani
- Chibuike Rotimi Amaechi
- Oladimeji Sabon Bankole
- John Kayode Fayemi
- Godswill Obot Akpabio
- Yemi Osinbajo
- Rochas Anayo Okorocha
- Yahaya Bello
- Tein Jack-Rich
- Christopher Onu
- Ahmad Lawan
- Ben Ayade
- Ikeobasi Mokelu
Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni a matsayin lokacin da za ta gudanar da zaben fid-da-gwani a tsakanin ’yan takarar nata don tsayar da wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2023.