A wani abu mai kama da yar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da su tattauna a tsakaninsu da nufin yin maslaha.
Shugaban Kasar ya fadi haka ne a lokacin da ya gana da masu neman takarar a daren Asabar a fadarsa dake Abuja.
- Takarar Shugaban Kasa Sai Dan Kudu –Gwamnonin APC A Arewa
- Za Mu Iya Hukunta Tinubu Kan ‘Gorin’ Da Ya Yi Wa Buhari —Adamu
“Ina kira a gare ku duka da ku tattauna a tsakaninku, da kuma tsakaninku da jam’iyya, da nufin kawo maslaha ta yadda za a taimaka wajen rage yawan masu sha’awar tsayawa takara da tsayar da gargarabadau a cikinku da kuma rage rashin tabbas a zukatan ’yan jam’iyya”, inji Buhari.
Haka kuma, duk da sanar da dakatar da wasu daga cikin masu neman takarar, Shugaba Buhari ya ce kwamitin tantancewa na jam’iyyar ya gamsu da cancantar kowannensu.
“Gabanin Babban Taronmu, jam’iyya ta tantance ta kuma gamsu cewa dukkan masu son tsayawa takara sun cancanta.
“Ganin haka sai Kwamitin Tantance Masu Son Tsayawar ya bayar da shawara cewa a kara kaimi a yunkurin samar da maslaha ta hanyar tuntubar juna”, inji Buhari.
A baya dai Shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin APC da sauran ’yan jam’iyya su taimaka mishi ya zabo mataimakinsa, lamarin da ya jefa zullumi a zukatan wasu masu sha;awar yin takarar.
Zaman zullumi
Wasu masana ma na ganin wannan magana ce ta tunzura Asiwajo Bola Ahmed Tinubu ya furta kalaman da wasu suke ganin cin fuska da gori ne ga Shugaba Buhari, ko da yake na hannun mai neman takarar sun musanta haka.
A ranar Asabar din wasu daga cikin gwamnonin APC a Arewa sun yi taro inda suka yanke shawarar cewa kamata ya yi dan takarar jam’iyyar ya fito daga Kudu.
Sai dai kuma a jawabin nasa Shugaba Buhari bai fadi matsayinsa game da bukatar gwamnonin ba.
Shugaban Kasar ya ce za a ci gaba da tuntubar juna don samo maslaha kafin Babban Taron Kasa da APC za ta yi ranar Litinin.
“Wannan ce [ganawa] ta biyu a jerin [tarurrukan tuntubar juna da nake yi] kuma na zaku na gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyya.
Maslaha da tuntubar juna
“Ana daukar wadannan matakai ne don tabbatar da hadin kan jam’iyya da kasancewarta tsintsiya madaurinki daya da kuma samar da jagoranci.
“Daya daga cikin abubuwan da na shaida wa Gwamnonin APC shi ne bukatar da ake da ita ta ganin jam’iyyarmu ta tunkari zaben Shugaban Kasa na 2023 da karfinta, kuma kanta a hade, sannan ta gabatar da dan takarar da zai bai wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa da kykkyawan fata.
“Ku ma masu girma ina yi muku irin wannan tunin”, inji shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kara da cewa yana sane da zaman zullumin da ’yan jam’iyya suke yi, don haka, “ina kira a gare ku da ku fahimci muhimmancin zaman lumana da hadin kan jam’iyya – wannan ba sai an fada ba.
“Bugu da kari, ina son tuna muku cewa wajibi ne wanda za mu zaba ya rike mana tuta ya zama gagarabadau, mai farin jini a wajen kowa kuma wanda zai iya hada kan kasa sannan ya magance manyan kalubalen da ke gabanmu”.
Tun bayan da PDP ta fitar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubajar a matsayin dan Takara jam’iyyar ta APC ta fada cikin rudani, kuma har yanzu babu alamun an warware an gano bakin zaren.