Allah Ya Yi wa Mai Martaba Sarkin Biu Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu rasuwa.
Sarkin ya rasu ne a daren Talata a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Mai Umaru an haife shi a ranar 9 ga watan Nuwambar 1940 a Biu da ke Jihar Borno a yanzu.
Ya halarci Karamar Firamare ta Kwaya Kusar a tsakanin 1947 zuwa 1949, sai Biu Central Primary daga 1950 zuwa 1953.
Marigayin ya kuma halarci Makarantar Hausari da ke Maiduguri daga 1953 zuwa 1955.
Ya kasance ma’aikaci a Asibitin Dabbobi a 1958, kuma shi ne Wakilin Masarautar Biu a Ma’aikatar al’adun gargajiya ta Jihar Borno.
Ya kuma taba zama Hakimin Birnin Biu daga 1975 zuwa 1989 kafin daga bisani ya zama Sarkin Kasar Biu.
Majiyar Aminiya ta rawaito cewa babban dan marigayin Maina Mustapha Mai Umar, kuma Hakimin garin Biu, ya ce Mai Martaba ya rasu ya bar mata 4 da ’ya’ya sama da 70 da jikoki 200.
Allah Ya ji Kansa da gafara.