Masarautar Ningi na daya daga cikin masarautu shida da ake da su a Jihar Bauchi, da ke Arewa maso gabashin Najeriya.
Akwai kabilu da yawa a masarautar, fitattu cikinsu su ne Ningawa, da Warjawa, da Ari da kuma Burra.
Haka kuma akwai kabilun Fa’awa, da Fulani da Butawa da Sirawa.
Mafi yawan al’ummar masarautar musulmi ne, kuma akwai Kiristoci da ma masu addinin gargajiya, haka kuma al’adun masarautar sun kasance kamar yadda addinai suka shimfida ne.
Akwai wuraren Tarihi guda uku a masarautar da suka hada da tsohuwar Garin Ningi, da tsohon masallacin da ke Duwo da kuma filin yaki da ke Tifi inda aka gwabza tsakanin Sarkin Kano Alu da Sarkin Ningi Usman danyaya.
Shi dai wannan masarauta ta Ningi wasu malaman addinin musulunci ne suka kafa shi a karni na 18 karkashin jagoranci wani malami da ake kira mallam Hamza.
Tarihi ya nuna cewa shi mallam Hamza ya yi kaura ne daga kasar Kano tare da wadansu malamai su kusan 40 saboda ya ki amincewa da ya rika biyan wani kudi da ake kira kudin raya kasa da masarautar Kano karkashin jagorancin sarkin Kano Muhammadu Bello ya sanya su rika biyan masarautar.
Lokacin da ya baro daga kasar Kano, ya fara zama ne a wani gari da ake kira Mara cikin kasar Lame a karamar Hukumar Toro cikin shekarar 1827.
A wani kaulin kuwa, Mallam Hamza ya taso ne daga garin Kano kuma ya fara sauka a wani gari da ake kira Ciru Basha cikin kasar Hakimin Burra, daga bisani ya zarce zuwa wani gari da ake ce kira Duwa.
Mallam Hamza ya yi amfani da ilimin addininsa wajen jawo hankalin kabilun Butawa da Warjawa da Kudawa da kuma Sirawa inda suka kulla amana kuma suna biyansa Jizya.
Kasancewar wadannan kabilu karkashinsa sai masarautun Zazzau da Bauchi da Kano suke masa kallon mai barazana garesu. haka ya sa aka kawo masa hari aka kasha shi amma al’ummarsa suka ci gaba da kasancewa a dunkule.
Da suka hadu sai suka zabi Ahmadu ya zama sarkinsu a shekarar 1850. Sarki Ahmadu ya shekara biyar zuwa 1855 Allah Ya yi masa rasuwa. Bayan sai sarki Abubakar dan Maje.
Yana da runduna mai karfi har ana yi masa kirari da dan Maje mai Tagwayen Masu dan Maje Mai Tabaryar Mashi.
Yayin da dan maje ya ci gaba da yaki da mamayar kabilu abin ya yi girma har masarautar Bauchi ta ga cewa ya kamata a yi wani abu don a hana dan Maje kar ya mamayi Bauchi, saboda hakane Sarkin Bauchi Ibrahimu ya kafa garin kafin Madaki inda aka bashi umurni da kada ya yaki dan Maje amma ya sa ido duk lokacin da ya yi wani yunkuri zai yaki Bauchi ya kai rahoto.
dan Maje Ya shekara 15 yana sarauta, kuma ya rasu a shekarar 1870, Bayan rasuwarsa sai Sarki Haruna karami ya gajeshi, ya yi shekara hudu a sarauta, da ya rasu sai Abubakar Gajigi ya gajeshi inda shi ma ya yi shekara hudu. Da ya rasu sai Usman danyaya ya karbi mulki. Bayan danyaya ya shekara biyu ne Turawa suka zo, da ya samu labarin Turawa sun iso sai ya yi hijira ya tafi kauyen Sama da ke kasar Hakimin Burra sai ya bada umurni aka harbeshi da kibiya ya rasu.
Bayan danyaya ya rasu sai aka nada Sarki Mamuda Haruna karkashin mulkin Turawa a matsayin sarkin da ke kula da kasashen Ningi, da Ari da Warji da kuma kasar Burra, inda ya yi shekara uku. A 1905 sai aka raba wadannan kasashen hakimai guda hudu Mamuda ya zama Sarkin Ningi, a shekarar kuma aka saukeshi a sarauta aka nada mallam Musa, sannan kuma aka sake nada Mamuda sarki a 1908, inda ya yi shekara bakwai yana sarauta sannan aka sake sauke shi aka kai shi Ilori a 1915.
Sai aka nada Sarki Abdu a 1915zuwa 1922, da ya rasu aka nada Sarki Zakari Shekara, inda ya shekara daya. Bayan ya rasu sai aka nada Adamu danyaya, wanda ya yi shekara 32 yana sarauta, ya rasu a 1955 sai aka nada Sarki Haruna S Datti na biyu, wanda ya shekara biyu zuwa 1957. Da ya rasu sai aka nada sarki Abdullahi Adamu shi ma ya shekara hudu, ya rasu a 1961. Sai aka nada sarki Ibrahim Gurama wanda ya yi mulki daga 1963 zuwa 1977. Sai sarki na yanzu Muhammadu Yunusa danyaya ya karbi mulki, wanda yanzu ya kai shekara 40 yana sarauta.
Ningawa sun kaura daga Tsohuwar garin Ningi zuwa sabuwar Ningi yau kimanin shekara 171 domin samun saukin matsalolin rayuwar.
Yanda ake zaben sabon sarki a masarautar Ningi
Mutane shida ne masu zaben sabon sarki a masarautar Ningi,sun hada da Madakin Ningi, da Sarkin Ari, da Hakimin Burra, da Hakimin Warji, da Limamin Ningi, da Shugaban karamar Hukumar Ningi, ko da yake Shugaban karamar Hukuma ba ya cikin masu rike da sarautar gargajiya.
Bayan an zabi sabon Sarki akan bashi abubuwa guda uku: Alkurani, da mashi da wadansu takalma da ake kira Simbatse, Madaki ke mika wa sabon sarki Mashi, da Simbatse Liman kuma ke mika masa Alkur’ani.
Yadda ake zaman fada a masarautar Ningi kuwa shi ne: Madaki ke gaba, sai Chiroma, sai Hakimin Nigi, sai Sarkin Burra, sai Sarkin Warji, sai Matawalle, sai Yarima, sai Baraya sai Sarkin Malamai, sai daniya, sai Tafida sai Shettima sai dangaladima.
Mai Martaba Sarkin Ningi na Yanzu Alhaji Yunusa Mohammed danyaya sarki ne mai daraja ta daya da alummarsa ke kaunarsa saboda adalcinsa.
An haifi Sarkin Ningi na 15 Alhaji Yunusa danyaya a 1935 a garin Ningi. Kuma shi ne Sarki na biyu daga gidan Malam Muhammadu Ciroman Ningi dan fitaccen mayakin nan Usman danyaya.
Ya yi firamare a garin Ningi daga nan ya halarci makarantar Midil ta Bauchi, sai Makarantar Koyon Aikin Tsabta (School of Hygiene) da ke Kano kafin ya je Jami’ar Ahmadu Bello inda ya yi difloma kan harkokin mulki.
Ya zama wakili a Majalisar Masarautar Ningi daga 1956 zuwa 1960, kuma ya zama Hakimin cikin Ningi kuma Chiroman Ningi daga 1959 zuwa 1960, kuma ya yi aiki a En’e ta Ningi da sauran hukumomin tsohuwar Jihar Arewa.