Al’ummomin yankunan Kolmani, yankin da aka gano danyen mai a tsakanin jihohin Gombe da Bauchi, sun bayyana fargabarsu kan jita-jitar canza wa rijiyar man waje daga inda aka kaddamar da ita.
A watan Nuwamban 2022 ne dai tsohon Shugaban Kasa, marigayi Muhammadu Buhari ya kaddamar da rijiyar man fetur ta farko a arewacin Najeriya sannan Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayar da lasisin ci gaba da hakar mai a wajen.
To said ai daga bisani aikin ya tsaya, kuma har Buharin ya sauka daga mulkin ba a ci gaba da aikin ba.
- Tuwon alkama da miyar kuka ne abincin da Buhari ya fi so – Hadi Sirika
- Na cika kashi 85% na alƙawuran neman zaɓe – Gwamna Abba
To sai dai Kwamishinan Makamashi da Ma’adinan Kasa na jihar Gombe, Sunusi Ahmad Pindiga, wata kwakkwarar tawaga daga jihohin Bauchi da Gomben sun ziyarci yankin na Kolmani, inda suka ba mazauna yankin tabbacin ci gaba da aikin.
Ya ce ziyarar ta ranar Alhamis ta biyo bayan korafin da mutanen suka kai tare da nuna damuwarsu a kan lamarin tare da neman ɗauki.
Kwamishinan ya ce, “Lokacin da na ji ƙorafin nasu, sai na kira Manajan wajen, inda ya buƙaci mu zo mu kawo ziyayar gani da ido, wanda hakan ne ya sa na tuntubi Kwamishinan Ma’adinai na jihar Bauchi. Mun je wurin da ƙwaƙƙwarar tawaga daga Bauchi da Gombe.
“Sun ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa za a canza wa aikin waje. Sun shaida mana cewa rijiyar da ake maganar yi a wani wajen wata karama ce, kuma ba dauke wannan za a yi ba, ita tana nan,” in ji Kwamishinan.
Ya kuma ce tuni har an haka ƙaramar rijiyar da zurfinta ya kai kimanin mita 10,000, yana mai cewa an kuma share filaye biyu a kusa da inda babbar rijiyar take kuma nan ba da jimawa ba za a fara amfani da ita.
Pindiga ya kuma ce akwai ƙananan rijiyoyi biyu a jihohin na Gombe da Bauchi da su ma aka kammala aikin haka su, “kuma komai yana tafiya daidai kamar yadda aka tsara”, in ji shi.
A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin dawo da aikin domin ganin an fara haƙar man nan ba da jimawa ba.
Kazalika, Ministan Man Fetur, Heinekan Lokpobiri, ya ce Najeriya ta ƙara adadin man da take haƙowa a kullum a yanzu daga ganga miliyan ɗaya zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas.
Sai dai ya ce ƙasar na hankoron ganin ta fara haƙo ganga miliyan biyu a kullum, kuma tana so rijiyoyin na Kolmani su ma su taimaka wajen haƙar wannan adadin.