Masarautar Muri da ke Jihar Taraba ta yau masarauta ce da ta samo asali a 1817 a karkashin al’ummar Fulani.
Daga 1892 zuwa 1893 daular ko masarautar ta kasance cikin yankin da Turawan mulkin mallaka na Faransa ke ikirarin mulka a karkashin gwamnan wancan lokaci, Louis Mizon.
A 1901 daular ta kasance daya daga cikin dauloli dubu 25 da 800 da Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka mulka lokacin da suka samu nasarar shiga Najeriya da mamaye kasar sakamakon rikici a tsakanin kasashen Turawan kan yankunan da kowannensu ke son mallaka don gudanar da tasa mamayar.
Kasar Muri ta kasance kasa mai dimbin albarkatun noma da kiwo. A wancan lokacin kafin kwace yanki ko Daular Muri da Fulani suka yi daga wurin wasu kabilu da suka hada da Mumuye da Kona da Jukunawa, yankin da yau ake kira da yankin Muri ya kasance maraya inda kabilu da yawa suke ikirarin mallakarsa.
Bayan gumurzu da kabilar Fulani wadanda asalinsu ya nuna cewa sun fito ne daga Gombe suka yi da sauran kabilu a yankin kuma daga baya suka samu nasarar kwace yankin kuma suka kafa daula a karkashin Daular Sheikh Usman Bin Fodiyo (RA) a 1817.
Hamman Ruwa dan Usman wanda ya fito daga tsatson Malam Buba Yaro na Gombe ne ya kasance Sarki na farko da ya mulki masarautar a tsakanin 1817 zuwa 1833 Miladiyya. Bayan marigayi Lamido Hamman Ruwa dan Usman an yi sarakuna da dama a masarautar wadanda suka hada da Lamido Ibrahim dan Hamman Ruwa wanda ya yi sarauta a tsakanin 1833 zuwa 1848.
Bayansa kuma sai Lamido Hamman dan Hamman Ruwa, wanda ya yi sarauta a tsakanin 1848 zuwa 1861. Bayansa sai Lamido Hamadu dan Bose wanda ya yi sarauta a tsakanin 1861 zuwa 1869.
A shekarar 1869 bayan rasuwar Lamido Hamadu dan Bose an yi Lamido Burma dan Hamman a tsakanin 1869 zuwa 1873. A tsakanin 1873 zuwa 1874 an yi Lamido Abubakar dan Hamman Ruwa. A 1874 zuwa 1897 an nada Lamido Muhammadu Nya dan Abubakar a matsayin Sarki. A 1897 zuwa 1903 Lamido Hassan dan Muhammadu Nya ya yi nasa sarautar.
Sai kuma a 1903 zuwa 1953 Lamido Muhammadu Mafindi dan Muhammadu Nya ya yi sarautar Muri. Lamido Muhammadu Tukur dan Muhammadu Nya ne ya zama Sarkin Muri daga 1953 zuwa 1965. Sarkin Muri Umaru Abba Tukur ne ya yi sarauta a tsakanin 1965 zuwa 1986.
A 1988 aka nada Sarki Abbas Njidda Tafida a matsayin Sarkin Muri, wanda saboda rikicin sarautar a tsakanin mutanen masarautar kan wanda zai gaji Umaru Abba Tukur, ya sa ba a bai wa Sarki Abbas sandar sarauta ba sai bayan shekara 18 wato a shekarar 2006.
Masarautar Muri a halin yanzu tana daga cikin manyan masarautun Jihar Taraba.
Mun ciro wannan tarihi ne daga shafin bakandamiya.com