Daular Usmaniyya ta Sakkwato, babbar daula ce a Yammacin Afirka da aka kafa fiye da shekara 200, inda ake kiran Sarkin Daular da Sarkin Musulmin Najeriya.
Gidan Rediyon BBC ya duba tarihin Daular Usmaniyya tare da tattaunawa da Masanin tarihi Kwamred Bello N. Junaidu, da Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan danbaba, wadanda suka amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aika masa.
Dangantakar Masarautar Sakkwato da Addinin Musulunci
Kwamred Bello N. Junaidu ya amsa ta da cewa alakar masarautar Sakkwato da addinin Musulunci ta samo asali ne saboda Mujaddadi Shehu Usaman dan Fodiyo, a lokacin da aka yi masa mubaya’a bayan Musulmi sun yi hijira daga garin Degel zuwa Gudu a 1804 a cikin watan Fabrairu saboda tsananin mulkin Sarkin Gobir na wancan lokacin, (shekara sama da 200 da suka gabata).
Ya ce: “Don haka za a iya cewa Musulunci ne ya kafa Daular Sakkwato sanadiyar Shehu Usman dan Fodiyo bayan an yi jihadi, amma masana tarihi sun ce tun kafin zamaninsa, an yi sarakuna na Musulunci a kasashen Hausa.
“Don haka Musulunci ne ya kafa daular ba sarauta ba. Bayan da Musulmi suka yi hijira ne zuwa Degel, sai suka zauna suka tattauna suka ga ya dace su zabi shugaba ko Jagora. To a nan ne suka ga ya dace Shehu Usman dan Fodiyo ya zama shugaba ko Amirul Muminin ko kamar yadda ake cewa da Fulatanci “Lamido Julbe,” inji shi.
“A lokacin an ce Shehu Usman dan Fodiyo ya ki amincewa da bukatar, sai da aka dauki lokaci sannan ya amince ya zama Sarkin Musulmi amma da sharadin cewa zai yi rawani da kur’ani da Hadisin Manzo (SAW). A kan haka ne ya amince a yi masa mubaya’a amma da Al kur’ani da Hadisi, kuma daga lokacin ne aka fara kiran Shehu Usman dan Fodiyo Sarkin Musulmi.”
“Daga nan ne Sarautar Sarkin Musulmi ta samo asali, duk wanda aka nada to ya zama Khalifan dan Fodiyo,” inji shi.
Me ya sa Sakkwatawa ke rantsuwa da rawanin dan Fodiyo
Kwamred Junaidu ya ce:
“Don Rawanin Sarkin Musulmi”, “Don darajar Rawanin dan Fodiyo,” wadannan nan su ne ire-iren rantsuwar da wadansu Sakkwatawa ke yi, ba wai don rawanin ba sai don kur’ani da Hadisi da rawanin ya dogara a gare su.
Don haka idan Basakkwace ya ce “Don rawanin Sarkin Musulmi”, yana nufin don “darajar kur’ani da Hadisi,” inji Kwamared Junaidu.
Tsarin sarautar Sakkwato kafin dan Fodiyo
Kafin Shehu Usman dan Fodiyo, Sakkwato na karkashin mulkin Gobir ne kuma a wancan lokacin ana mulki ne na sarauta, wanda kuma ba bisa tsarin Shari’ar Musulunci ba, mulki ne na gado daga kaka da kakanni.
Mulki ne na gargajiya kafin zuwan Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo.
An samu sauyi lokacin da Musulmi suka yi wa dan Fodiyo mubaya’a, tun kafin ma a fara jihadi inda aka jaddada Musulunci a kasashen Hausa 10 irin su Zazzau da Kano da Bauchi da aka bai wa tuta, dukaninsu kuma suka dawo karkashin Daular Sakkwato.
A ina dan Fodio ya fara kafa tuta?
A yankin Gudu a Jihar Sakkwato, a nan ne Shehu Usman dan Fodiyo ya fara kafa tuta inda Musulmi suka yi masa mubaya’a bayan ya yi hijira daga mulkin Gobir.
A lokacin ma an ji dan Fodiyo yana cewa “Gudu yau ba Gudu,” wato an kai iyaka, za a tsaya ba wani gudu domin kare addinin Musulunci.
Masana tarihi sun ce, Musulmi sun ci gaba da yin kaura zuwa garin Gudu saboda dan Fodiyo, kuma a nan ne aka kaddamar da jihadi.
Masarautu nawa dan Fodiyo ya ci da yaki?
Masarautu da dama ne Shehu Usman dan Fodiyo ya ci da yaki, tun daga Najeriya zuwa Nijar da Burkina Faso da Jamhuriyar Benin.
A Najeriya daulolin da dan Fodiyo ya ci da yaki sun kai 18.
Kuma ya fara ne tun daga yankin Sakkwato, kamar Sarkin Kabbin Yabo Muhammadu Mauje da aka ba tuta har zuwa Zamfara da ’Yan Doto da Katsina da Adamawa da Ilori da Nupe da Bauchi.
Akwai kuma Jama’are da Misau da Hadeja da Kazaure, duk wadannan wurare ne da dan fodiyo ya jaddada addinin Musulunci, kuma aka samu sauyi aka kafa masarautu na addini.
Khalifa na farko bayan rasuwar dan Fodiyo
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, shi ne Khalifa na farko bayan rasuwar Shehu Usman dan Fodiyo, wanda dansa ne da ya yi shugabanci bayan mahaifinsa, a tsawon shekara 20, daga 1817 zuwa 1837.
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya ci gaba da shugabanci a irin tsari na mahaifinsa Shehu Usman dan Fodiyo domin jaddada dorewar Daular Usmaniyya.
A zamaninsa ne aka yi yakin Gobirawa da Zamfarawa da suka kawo wa Sakkwato hari, amma duka ya ci su da yaki domin kare Daular Usmaniyya.
Shin gidan Sarautar Sarkin Musulmi kashi nawa ya rabu?
Gidan Sarautar Sarkin Musulmi a Sakkwato ya kasu ne gida biyar, wato ’ya’yan Shehu Usman dan Fodiyo. Gidan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Akwai gidan Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Mai Katuru wanda kabarinsa ke Katuru a cikin yankin Shinkafi cikin Jihar Zamfara. Sai gidan Ahmadu Rufa’i wanda zuriyarsa ke Silame da gidan Muhammadu Buhari wanda zuriyarsa ke rike da garin Tambuwal da Dogon Daji da Sifawa. Sai Isa Autan Shehu, wanda shi ne na karshe daga cikin ’ya’yan Shehu Usman dan Fodiyo maza guda 20, kuma zuriyarsa ce ke rike da garin Kware.
Gidan da bai taba Sarautar Sarkin Musulmi ba
Sarautar Sarkin Musulmi ba ta taba fadawa a gidan Ahmadu Rufa’i dan Shehu, Sarkin Musulmi na bakwai ba. Kuma tun lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa a 1873, zuriyarsa ba su sake karbar Sarautar Sarkin Musulmi ba.
Haka ma gidan Isa Autan Shehu bai taba rike Sarautar Sarkin Musulmi ba. Amma ’ya’ya da jikokin gidan Bello da Atiku dukaninsu sun yi Sarautar Sarkin Musulmi.
Wane Sarkin Musulmi ne ya fi dadewa?
Marigayi Abubakar na III, Sarkin Musulmi na 17 ne ya fi dadewa a Daular Usmaniyya, wanda ya shafe shekara 50 yana mulki daga 1938 zuwa 1988.
Abubakar na III jika ne ga Mu’azu Sarkin Musulmi na tara, daga gidan Sarkin Musulmi na biyu Muhammadu Bello.
Abubakar na III shi ne mahaifin marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido da Sarkin Musulmi na yanzu Sa’ad Abubakar.
Shin da gaske ne Ibrahim Dasuki dan mace ne?
Ibrahim Dasuki ne Sarkin Musulmi na 18, wanda shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nada bayan rasuwar Abubakar na III.
A lokacin an yi hatsaniya a Sakkwato inda har wadansu ke danganta Ibrahim Dasuki a matsayin dan mace da bai cancanta ya zama Sarkin Musulmi ba.
Amma gaskiyar (magana) Ibrahim Dasuki ya fito ne daga gidan Muhammadu Rufa’i dan Shehu Usman dan Fodiyo.
Halliru ne mahaifin Dasuki, shi kuma dan Abdullahi Bara’u, shi kuma dan Muhammadu Buhari, shi kuma dan Usman dan Fodiyo.
Zuriyar su Dasuki ne suka kafa garin Tambuwal da Dogon Daji da Sifawa.
Dangantakar Sarkin Musulmi da Masarautar Maradun
Gidan Sarautar Maradun gidan Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi na biyu bayan Shehu Usman dan Fodiyo.
Mu’allayidi dan Sarki Muhammadu Bello ne ya kafa Masarautar Maradun. Kuma dan gidan sarautar Maradun zai iya neman Sarautar Sarkin Musulmi. Sai dai kuma watakila yanzu da aka raba Jihar Zamfara daga Jihar Sakkwato, yana da wahala a samu wani daga gidan Sarautar Maradun a matsayin Sarkin Musulmi, kamar misalin gidan Sarkin Kwantagora a Jihar Neja wanda ’ya’yan gidan Sarkin Musulmi Atiku ne.
Ko akwai Yarima Mai jiran Gado a Sakkwato
Magajin Gari Alhaji Hassan danbaba ya amasa tambayar da cewa: “Babu Yarima Mai jiran Gado a tsarin masarautar Sarkin Musulmi.
“Idan har sarauta ta fadi, manyan sarakunan majalisar Sarki ke zaunawa su zabo sunaye daga gidajen gidan Shehu Usman dan Fodiyo.”
Su wa ke zaben Sarkin Musulmi?
“Wadanda ke da alhakin zaben sabon Sarkin Musulmi guda 11 ne da ake kira Sarakunan Karaga. Kuma cikinsu babu wani wanda kai-tsaye dan uwa ne ga dan Fodiyo.
Sarakunan sun hada da:
1.Wazirin Sakkwato
2.Magajin Garin Sakkwato
3.Magajin Rafin Sakkwato
4.Galadiman Gari
5.Sarkin Yakin Binji
6.Sarkin Kabin Yabo
7.Ardon Dingyadi
8.Baraden Wamakko
9.Ardon Shuni
10. Sa’in Kilgore
11.Sarkin Adar na dundaye
“A duk lokacin da Sarauta ta fadi su suke zaunawa su zabi sabon Sarkin Musulmi,” in ji Magajin Gari Alhaji Hassan danbaba.
Shin Zuriyar dan Fodiyo kawai ake binnewa a Hubbare?
Kamar yadda Hubbare makaranta ce da mutane ke zuwa daukar karatu zamanin Usman dan Fodiyo, haka za a iya rufe kowa a hubbaren saboda dangantakar Shehu Usman dan Fodiyo da addinin Musulunci.
Akwai kaburburan mutane da dama wadanda ba su da alaka da dan Fodiyo illa ta addini.
Wadansu da dama kan bar wasiyyar neman alfarma a binne su a Hubbaren Shehu, ba lallai sai zuriyar Mujaddadi ba.
Wannan tarihi ne da Gidan Rediyon BBC ya rairayo bayan masu sauraro sun aike masa da tambayoyi a kan tarihin Masarautar Sakkwato wanda Awwal Ahmad Janyau ya rubuta.