✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takaitaccen tarihin limaman Sallar Tarawih a Masallacin Harami a bana

A watan Azumin Ramadan mai kamawa limamai shida ne Gwamnatin Kasar Saudiyya ta ayyana domin jagorantar sallolin Tarawih da Tahajjud a Masallacin Haramin Makkah. Ga…

A watan Azumin Ramadan mai kamawa limamai shida ne Gwamnatin Kasar Saudiyya ta ayyana domin jagorantar sallolin Tarawih da Tahajjud a Masallacin Haramin Makkah.

Ga muhimman abubuwan da muka rairayo muku a takaice game da limanan sallolin na Kiyamullaili:

Limaman Masallacin Haramin Makkah tare da wasu Limaman Masallacin Madinah bayan taro kan sallolin Tarawih da Tahajjud (Hoto: @hsharifaininfo).
 1. Sheik Abdul Rahman Al-Sudais
 • Sheikh Sudais shi ne babban Limamin Masallacin Haramin Makkah
 • Shi ne kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Masallatan Haramin Makkah da Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina.
 • An haife shi ranar 10 ga watan Fabrairu, 1960 a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya
 • Yana da mata daya, sunanta Fahda Ali-Raouf kuma Allah Ya azurata shi da da daya, Abdullah bin Abdul Rahman Al-Sudais.

 

 1. Sheikh Saud Al Shuraim
 • Sheikh Shuraim Farfesa ne a Fannin Shari’a da Darussan Musulunci a Jami’ar Umm Al-Kura da ke garin Makkah.
 • Baya ga kasancewarsa gangaran a haddar Al-Kur’ani, Sheikh Shuraim mai aikin yada da’awar Musulunci ne
 • An haife shi a ranar 19 ga Janairu, 1964, a birnin Riyadh, kasar Saudiyya
 • Ya kammala giriinsa na farko a Jami’ar Umm Al-Kura a 1995
 • Yana daya daga cikin manyan limaman Sallar Juma’a a Masallacin Haramin Makkah
 • Sunansa na ainihi Saud ibn Ibrahim ibn Muhammad Al-Shuraim.

 1. Abdullah Awad Al Juhany
 • An haifi Sheikh Juhany ranar 13, ga watan Janairu 1976, (Shekaru 45), a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
 • Ya yi digirinsa na farko a kan Ilimin Al-Kur’ani Mai Girma a Jami’ar Musulunci da ke Madina, digirinsa na uku kuma a Jami’ar Ummul Kura da ke Makkah.
 • Sheikh Juhany daya ne daga cikin manyan Limamai a Masallacin Haramin Makkah Mai Alfarma.
 1. Maher Al Mueaqly
 • An haifi Sheikh Maher Al Mueaqly ranar , ga Janairu, 1969 a birnin Madina
 • Sunan mahaifiyarsa Sa’imah bint Mahmud Al-Sisi, mahaifinsa kuma Hamad Bin Muiqal Al Muaiqly
 • Yana daga cikin manyan limamai a Masallacin Haramin Makkah da Masallacin Madina
 1. Sheikh Bandar Baleelah
 • Haifaffen birnin Makkah ne a 1975
 • Sunansa Bandar bin Abdulaziz bin Siraj bin Abdul Malik Baleelah
 • Ya yi digirinsa na farko a Makkah, inda ya kammala a 1996
 • Ya kammala Digirinsa na biyu a Jami’ar Ummul Kura a 2002
 • Digirinsa na uku kuma a 2008 a Jami’ar Musulunci da ke Madina
 • Ya zama limamin wucin-gadi mai jagoranci Sallar Tarawih a Masallacin Haramin Makkah a watan Ramadan, shekarar 2013.
 • Cikin wata uku kuma ya zama Babban Limami cikakke a masallacin
 • Sheikh Bandar, Farfesa ne a Tsangayar Shari’ah a Jami’ar Da’if
 • Sheikh Bandar ya wallafa littafi kan Sallar Rokon Ruwa a 2016
 1. Yasser Al-Dosari
 • Sunansa Yasser Ibn Rashed Ibn Houseine Al Ouadaani Al Dossari
 • An haife shi a 1980 a unguwar Al-Kharj da ke Riyadh a Saudiyya
 • Ya yi karatu a Jami’ar Musulunci ta Imam Muhammad Ibn Saud da ke birnin Riyadh