Da sunan Allah Mai rahma Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode MaSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa. Muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne. (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), mafi kyawun shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu (Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi wanda aka kirkira a cikin addini, kuma duk abin da aka kirkira a cikin addini bata ne, wanda karshensa wuta. Allah Ya tsare mu daga gare ta, amin.
Yau, cikin yardar Allah, makalarmu za ta gudana ne a kan hassada da illolinta da kuma wasu daga cikin magungunanta. Bayanin dai zai kasance a takaice, wato kamar dai manuniya ce ga mai karatu don hankalinsa ya jawu kan al’amarin, ya gane illarsa da maganinsa, idan ya fada cikinsa. Allah Ya kiyashe mu da sharrin hassada da mahassada, amin.
Ma’anar hassada ita ce ganin kyashi; nunkufurci; kiyayya. Wanda ake wa hassada shi ne mai abin hannu ko matsayi na addini ko na duniya. Abin da ya sa ake yin hassada shi ne rashin kyakkyawan tunani; izza; ji-ji-da-kai; son shugabanci ko isa; kazantar zuciya; mugunta; zalunci da mummunar dabi’a. Allah Ya tsare dukkan Musulmi daga gare ta.
Hassada ita ce mutum ya yi burin abin da yake wajen wanda ake wa hassadar na alheri na abin duniya ne ko addini, ya gushe. Wannan haramun ne, domin yana cutar da jiki da addini. Allah, saboda Ya nuna tir dinSa da wannan dabi’a da masu yin ta, sai ya ce: “Ko suna hassadar mutane ne a kan abin da Allah Ya ba su daga falalarSa? …. (An-Nisa’i: 54). Allah Mai girma da daukaka, Ya ja hankalinmu da neman tsari daga sharrin mai hassada, inda Ya ce, “Da sharrin mai hassada, idan ya yi hassada.” (Al Falak: 5).
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya gargade mu kan (matsalar) hassada da irin illar da ke tattare da ita, inda ya ce, “Kashedinku da hassada, saboda ita tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye kiraruwa.” Abu Dawuda ne ya ruwaito Hadisin.
Haka nan saboda ya sa al’ummar Musulmi ta kasance tabbatacciya, dunkulalla a waje daya ba tare da ta samu matsala ba, sai ya ja hankalinta ga Hadisin da Buhari ya ruwaito a cikin littafin Arba’una Hadis na Nawawiy – (Hadisi na 35).
Ana neman tsari daga mai hassada lokacin da ya bayyana mummunar manufarsa ta yin hassadar, lamarin da yana iya yin komai don ganin ya cimma gurinsa na mugunta.
Hassada iri uku ce: Ta daya, mutum ya ki falalar kuma ya yi gurin a dauke ta daga wanda aka yi wa ita ko da kowa ma zai rasa –wannan ta fi muni.
Ta biyu mutum zai yi burin falalar ta komo wajensa.
Ta uku, kodayake an kira ta hassada, amma a hakika tana da sunan tseratayya ne, wato mutum ya yi burin samun irin falalar, ba tare da an hana ma wanda aka ganta a wurinsa ita ba, domin ya yi aikin alheri kamar ko fiye da wancan mai falalar –wannan ana kiranta gabda ne a Larabci.
Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, a wani hadisi da Buhari da Muslim suka ruwaito, “Babu hassada, sai a cikin abubuwa biyu: Mutum mai dukiya da Allah Ya azurta shi da ita, kuma yana ba da ita sadaka –dare da rana; sai kuma mutumin da Allah Ya azurta da Alkur’ani yana karanta shi dare da rana.”
Me ke haifar da hassada?
1. kiyayya: Yawanci saboda rashin kaunar wanda ke da falalar, sai hassada ta darsu a zuciya. Wannan lamari yakan haifar da a aiwatar da munanan dabi’u na jiyar da rauni, wato jikkatawa ko ma kisa gaba daya.
2. Izza da ji-ji-da-kai: Raina kurar wanda aka ba falala kan sa haka, wato ganin cewa wai kamar bai isa a ba shi wannan matsayin ba ko dukiyar ko abin da ya yi kama da su. Kamar dai yadda kafirai suka yi hassada da Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma suka bukaci wai don me ba a ba wani babban mutum annabtar ba daga garuruwan Makka da da’ifa? (Suraru Zukhruf 31).
3. Son mulki da iko: Lamarin da kan sa a yi ta gogoriyon bankade juna, musamman in mutum yana ganin ya fi kowa kwarewa a kan abu kaza… ko kuma ya gane ana kwarzanta shi kan abu kaza, za ka iske ba ya son a ce wani ya fi shi, matukar dai zuciyarsa tana da cutar hassada.
4. Daskarewar zuciya da kaunarta ga mugunta da kazancewarta dangane da biye wa soye-soyenta a rayuwa, domin zuciya, an ce, ‘muguwar nama.’ Da yawa za ka samu mutumin da ba shi da wani iko a rayuwa ko matsayi, amma saboda munin zuciyarsa, misali idan an ambaci wani dagane da matsayinsa ko irin kyan halinsa, sai ya nuna nunkufurcinsa game da haka. Duk kirkinka da kyawun hali da dabi’a, ba ya yabawa, amma idan wani abin bakin ciki ya same ka, sai ya ji dadi, alhali wasu lokuta ba abin da ya hada ka da shi. Kodayaushe yana fatar mugun abu ga mutane, amma kuma ba ya kaunar wani alheri ya same su. Wannan mummunar dabi’a ce da ta haifar da mummunar hassada a cikin mummunar zuciya.
Illoli
Shi mai hassada yana cutar da kansa ta hanyoyi uku: Farko dai yana tara wa kansa zunubi saboda haramcin hassada.
Na biyu, mummunar dabi’a ce, wadda Allah ba Ya so, domin dabi’a ce ta kin falalar da Allah Ya yi wa bayinSa, yana nuna kiyayya ga abin da Allah Ya yi ko Yake yi.
Na uku, yana cutar da kansa saboda bakin cikin da yake tare da shi koyaushe da kuma damuwa da ganin kyashin abin da wani ya samu, ya rasa zaune da tsaye, yana ta dambarwa cikin dimuwar kaka-nika-yi da sauran nuku-nukun zuciya da jiki gaba daya.
Na hudu, bayan wadannan, hasada tana haifar da rashin hadin kai tsakanin al’umma.
Na biyar, hassada tana lalata kyawawan ayyukan mai ita, kamar dai yadda bayani ya gabata.
Sannan na shida, tana haifar da azabar kabari.
Magani
1. Yana daga cikin magungunan hassada, mutum ya ji tsoron Allah cikin duk al’amurransa, sannan ya guji son zuciyarsa.
2. Mutum ya yi kokarin fahimtar falalar Allah, wadda Yake bayar da ita ga wanda Ya so daga cikin bayinSa, wadda shi ma Allah Yana iya ba shi irinta ko ma abin da ya fi ta, saboda haka wurinSa ake nema.
3. Mutum ya nusar da zuciyarsa dangane da falalar da wani ya samu, kuma ya soyar da ita ko ya tilasta mata so da yarda da wanda aka ba ita, tare da kauda kai kan abin da waninsa ya samu.
4. Mutum ya yi aiki tukuru, ya mayar da al’amarinsa ga Allah, kuma ya roki Allah din Ya ba shi tasa falalar.
5. Mutum ya roki Allah Ya tsare shi da yin hassada kuma ya nemi tsari daga mahassada.