A mako mai zuwa ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emeifile, zai gurfana a gaban Majalisar Wakilai kan shirin takaita cire kudade.
Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Idris Wase ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, bayan ya jagoranci zaman kwamitin majalisar, inda ya ce Gwamnan CBN ya aike da wata takarda domin sanar da shi rashin zuwan majalisar.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne ake sa ran gwamnan na CBN zai bayyana a gaban majalisar.
Sai dai ya aike da sakon neman gafara saboda ba ya kasar a halin yanzu, amma zai bayyana a gaban majalisar da zarar ya dawo.
Majalisar ta amince da uzurin Emefiele, inda ta ce za ta sake ware masa rana don bayyana a gabanta.
Don haka ta umarci shugaban kwamitinta kan Dokoki da Kasuwanci, Abubakar Hassan Fulata da ya tattauna da gwamnan babban bankin don sanya ranar da zai sake bayyana.
Majalisar ta gayyaci Emeifile ne bayan kudirin da Magaji Da’u Aliyu ya gabatar a ranar Alhamis din da ta gabata kan kudurin CBN na takaita cire tsabar kudi.
Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ya bukaci gwamnan na CBN da ya bayyana don yi musu cikakken bayani game da tsarin da kuma irin tasirin da zai samar.
Tun da farko majalisar ta soki lamirin CBN na shigo da tsarin da zai takaita cire kudi, lamarin da ta ce zai jefa mutanen karkara cikin tsaka mai wuya.