A wannan mako za mu karkare maudu’in nan da ake ragargaza takaddama a tsakanin maza da mata, domin gano wadanda suka fi rikon amanar soyayya. A wannan makon ma ga sakonnin da muka samu:
Za mu bude ne da batun Fatima Abdullahi ’Yar Lajawa (08112538490) da take cewa: “Haba ’yan samari, ko kadan ban yi zaton akwai wanda zai furta koda harafi daya daga cikinku ba, idan ana batun alkawari bare wa ya fi rike alkawari. Da yawa daga cikinku kuna fita daga filin daga nan kuna komawa gefe kuna maganar wai daga yarinya ta ga mai kudi sai ta juya baya, wanda kuma hakan shaci-fadi ne da kokarin nade tabarmar kunya. Ba zan ce gaba daya ba, domin a ko’ina akan samu nagari da kuma gurbatattu. Ban jin zan yi kaffara idan na rantse cewa kashi 99.5 na maza ba su rike alkawari. Za ku yarda da ni, idan kuka dubi yadda maza suke rige-rige wajen cin amanar matansu. Wannan jarida Aminiya ta isa ta zama hujja da labaran da take bayarwa na irin cin amanarku a gare mu.”
Shi kuma Mukhtar (07066434519), ya biyo bayan ’Yar Lajawa da nasa batun, mai cewa: “Ko shakka babu duk sa’ar da aka ambaci amana ko kamun kai, duka dabi’u ne da a cikin maza da mata ana samun masu su da wadanda suka rasa hakan. Sai dai ni a nan na tsaya tsakiya, wato a duk sa’ar da aka ce mace wurin juriya da rike alkawari, to da dama sun cancanci a yaba su, domin kamar ra’ayin Mista Tsari, wanda ya fi kawo illolin maza da dama, haka yake. Haka nan ra’ayin Malam Ibrahim Hamisu Kano, shi kuma ya karkata ga bai wa maza shaidar rikon alkawari amma duka dai yau duk yadda ka dau mace kana yi mata hidimomi a matsayin matarka ta aure, koda a ce kana da iko kuma ka biya mata kudin kujera zuwa aikin Hajji, ta je ta sauko farali; to in da matsala da ita a tsakaninku za ta kaure, shi ne batun karo aure? Wato kana cewa ka yi niyyar auro abokiyar zama, to sai sa’a ta tuna alheranka na baya, bayan kuwa shi karin aure ibada ce, amma ita sam-sam, ita dai daga kai sai ita.
Ashe cewa wai maza na cin amana, ai da dama su ma tun a cikin neman auren maimakon duba kima da cancantar mai nema, a’a su dai inda za a ja kaya, duk da cewa inda za a ja kayan ba laifi inda hali mai kyau amma sau nawa ne mace ke zuwa gidan da ake kallo komai ya ji a ishe an yi wa rogo hangen kitse. Ai rikon amana da juriya dabi’a ce, a iya samu ga maza haka a iya samu ga mata, duka dai a yi wa juna adalci shi ne ya fi.”
Sai kuma ra’ayin Nabeela Pretty Kazaure (09035685131), tana cewa: “A gaskiya mata sun fi maza rike alkawari. Mace na iya zama da mijinta cikin halin talauci da rashin lafiya komai wuya amma da namiji ne sai ka ga ya kai ta gidan iyayenta, ya ce ta yi jinya a can. Za ka ga budurwa da saurayi na soyayya amma da ya hango wadda ta sha bilicin, ta yi fari sai ka ga ya fara zamewa ya koma wajen waccan. Sau tari ana samun mazan da suke soyayya kawai ta karya, wani sai ka same shi da budurwa ta kai hamsin amma a mata ba za a taba samu ba.”
Shi kuwa Basiru Suru Tudun Jukun Zariya (07067216922), a nasa batun, yana cewa: “A kan rike alkawari saboda in dai ka ga mace ta rike maka alkawari, ba ta guje ka ba, to ba shakka kana da wadata ne ko kuma kana yi mata duk wata hidimar da ta kawo maka. Duk da haka ko kana yi mata, da zarar ta hangi wani wanda ya fi ka hali ya zo, sai ta juya maka baya. Rike alkawari sai maza amma da akwai irinsu Hauwa, wadanda samun su zai yi wahala yanzu.”
Za mu karkare da sakon Abubakar A. Malanjo Gombe (07067758596), wanda ke cewa: “A gaskiya mata sun fi maza rike alkawari saboda idan kana nema da mace har ta ce ‘ina kaunarka’ to da gaske take yi. Sabanin mu maza, namu a baki yake, don namiji fa sai a hankali.”