Ga duk wanda ke bibiyar harkokin siyasar kasar nan daga lokacin da sojoji suka hadiye kwadayinsu na ci gaba da mulkin kasar a 1999, ya san cewa fakewa da ake yi da batun rikicin makiyaya da manoma ba komai ba ne illa nuna kiyayya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari don kawai yana cewa a bi gaskiya a matsayinsa na wanda ya fito daga tsatson Hausawa da Fulani.
Tabbatacce ne cewar an dade ana wannan rikici na Fulani makiyaya da manoma a bangarori daban-daban na kasar nan, amma ba a taba fitowa gadan-gadan ana nuna kiyayya karara ga wata gwamnati ba kan lamarin sai wannan gwamnati ta Buhari.
In mai karatu zai waiga baya lokacin gwamnatin Obasanjo kowa ya san lokuta da dama an samu rikici mai yawa a tsakanin makiyaya da manoma inda aka rika rasa rayuka da dukiyoyi a tsakanin bangarorin musamman a jihohin Bauchi da Filato da Yobe da Jigawa da Borno da Adamawa da Taraba da Binuwai, jihar da rikicin da aka yi a cikinta a bayan nan ke kokarin ta da kurar da wadansu ke son yin amfani da shi don kawo barazana ga hadin kan kasa. Masu maganganun cewa gwamnatin Buhari ce ke daure gindin rikicin suna nan a wancan lokacin amma sun gaza cewa komai don kawai shafaffe da mai ne da ya fito daga wani sashin kasar nan ke mulkarta.
Haka baya ga rikice-rikicen makiyaya da manoma a lokacin gwamnatin Obasanjo har ila yau lokacin takwaransa dan Kudu Goodluck Jonathan nan ma an yi ta hatsaniya a tsakanin makiyaya da manoma, musamman a jihohin Zamfara da Adamawa da Taraba da Nasarawa da Filato da Binuwai da wasu bangarorin Kudu aka yi ta kashe-kashe fiye da kima, inda a Jihar Binuwai kadai rikicin da aka rika yi ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa a tsakanin Fulani makiyaya da ’yan kabilar Tibi fiye da a yanzu, amma a wancan lokaci babu wani korafin rashin yin daidai daga wadancan mutane masu kokarin shafa bakin fenti ga gwamnatin Buhari na Jam’iyyar APC.
Hakan ya faru ne ba don komai ba sai don shi Jonathan din nasu ne da ya fito daga bangaren shafaffu da mai da ke da kafafen watsa labaran da kan iya mayar da fari baki don kin Allah da sunan kishin yanki da al’ummarsu.
Don haka an yi walkiya mun gane na duhu, manufa duk ma’abocin gaskiya ya san cewa, korafin da ’yan gaza gani ke yi cewa wai gwamnatin Buhari na jan kafa wajen kawo karshen rikita-rikitan da ake fama da ita a tsakanin makiyaya da manoma a wasu jihohi, musamman Jihar Binuwai da aka rasa rayuka kusan 70 ba komai ba ne illa son rai da nuna kiyayya ga gwamnatin ceton talakawawa ta Baba Buhari, gwamnatin da talakawa suka yi ta nema a tsawon lokaci domin kai su ga tudun mun tsira, inda ko a yanzu kwalliya ta biyan kudin sabulu.
Don haka masu cewa wai gwamnatin Buhari na jan kafa ko nuna goyon baya ga makiyaya a wannan hatsaniya, suna ina lokacin da ’yan kabilar Mambila a Jihar Taraba suka rika aiwatar ta kisan kare dangi ga makiyaya Fulani, inda aka kashe fiye da makiyaya dubu da dabbobi fiye da lissafi da gidaje fiye da 300, amma wadancan mutane su da kafofin watsa labaransu suka yi gum da bakunansu ba su ce komai ba?
Har wa yau wadancan mutane suna ina lokacin da kabilun bacama a Jihar Adamawa da ’yan kabilar Birom da makamantansu a Jihar Filato da kabilun Kudancin Kaduna da sauran yankunan kasa suka rika kashe makiyaya da dabbobinsu amma ba su komai ba sai a yanzu da suka ga lokacin siyasa ta kunno kai, suka gane cewa sun makara?
Don haka su sani sara da sassaka ba zai hana gamji ya yin toho ba. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, mafi yawan al’ummar kasar nan sun yi musu caffa, ganin cewar babu cuta babu cutarwa ga lamarin, tare da neman Shugaba Buhari ya amince domin sake tsayawa takara a zaben badi, don ci gaba da aikinsa na ceto kasa, musamman mu al’ummomin jihohin Arewa maso Gabas da muka yi fama da rikicin ’yan ta’addan Boko Haram, kuma sakamakon tsayuwar dakar Baba Buhari lamarin ke gab da zama tarihi.
Sani Chinade, [email protected] 08036526185.