Takaddama ta biyo baya a yayin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ke shirye-shiryen fitar da sakamakon karshe na zaben Gwamnan Jihar Kano.
Bayan karbar sakamakon kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar, Baturen Zaben, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, ya bukaci kimanin awa biyu domin tattarawa da lissafa alkaluman kafin sanar da sakamakon karshe.
- Zaben Gwamnan Kano: Jam’iyyar NNPP na gaban APC da kuri’a 128,897
- Abba Kabir Yusuf na NNPP na shirin zama Gwamnan Kano
Da haka ne za a tantance ko kuriun da aka soke ba su kai tazarar kuri’un da ke tsakanin manyan ‘yan takara a zaben.
Zai bibiyi rahotannin da turawan zaben kanan hukumomi suka gabatar, sannan yanke hukunci a kan zabukan da aka soke, bayan fayyace dalilan soke zaben.
Kafin nan, baturen zaben ya nuna wa wakilan jam’iyyu takardun da za a tattara sakamakon zaben na karshe, su shaida cewa babu komai a cikinsu.
Idan kuri’un da aka soke suka haura tazarar kuri’u 128,897 da ke tsakanin manyan ’yan takara, to akwai yiwuwar a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, kamar yadda ta faru a jihar a 2019.
Sai dai kuma, wakilan jam’iyyu na ce-ce-ku-ce kan yadda shi baturen zaben zai yi alkalanci a kan matsayin kuri’un da aka soke.
Aminiya ta gano baturen zaben rike da takardar dokar zabe, yana dubawa, haka shi ma wakilin jam’iyyar NNPP, Abdullahi Baffa Bichi.
A halin da ake ciki dai dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ne ke kan gaba da kuri’u 1,019,602, a yayin da mataimakin gwamna mai ci kuma dan takarar APC, ke biye da shi da kuri’u 890,705.
Baffa Bichi ya kalubalanci bukatar baturen zaben na komawa wani wuri domin tattara sakamakon na karshe, amma ya bayyana cewa yana bukatar lokaci da natsuwa da zai bi rahotannin abin da ya faru a rumfunan zaben, domin yanke hukunci gabanin sanarwar.
Yanzu dai ana jiran sanarwar INEC a hukumance.