✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddama kan tsawaita dokar ta-baci

Dalili da yadda aka samu rabuwar kawuna tsakankanin ’yan Majalisar Wakilai wanda ya jawo matakin dokar ta-baci da aka sanya a jihohi uku a yankin…

Dalili da yadda aka samu rabuwar kawuna tsakankanin ’yan Majalisar Wakilai wanda ya jawo matakin dokar ta-baci da aka sanya a jihohi uku a yankin Arewa-maso-Gabas ya cika, ba tare da tsawaita shi ba a hukumance.
Hatta Majalisar Dattijai ita ma kanta ya rabu kan ko ta amince da bukatar Shugaba Goodluck Jonathan na tsawaita dokar a karo na uku, bayan karewar wa’adinta a ranar 21 ga watan jiya. Jihohi uku da suka hada da Barno da Yobe da kuma Adamawa wadanda rikicin Boko Haram ya yi kamari wanda kuma ya tilasta daukar matakin, har yanzu ba su kai ga samun kwanciyar hankalin da aka hanga ba tun farko. Takaddamar da ta faru a Majalisar Dattijai ta zo ne bayan shafe kwanaki ana tattaunawa, ciki har da taro a asirce da manyan hafsoshin kasar nan.
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fara ayyana kafa dokar ta-bacin ne a jihohin uku, ranar 13 ga watan Mayun bara, bayan mayan hafsoshin sojin kasar nan sun bukaci yin hakan, inda suka ce daukar matakin zai taimaka wa sojoji samun nasara kan ’yan Boko Haram. Har ila yau, bayan cikar wa’adin dokar ne a watan Nuwamban bara, sai aka kara tsawaita dokar bayan samun amincewar majalisa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. An kara tsawaita wa’adin dokar a karo na biyu cikin watan Mayun bana, bisa hujjar sojoji su karasa yakin da suke da ’yan Boko Haram da kuma dawo da kwanciyar hankali a jihohin da rikicin ya shafa. Kodayake, watanni 18 bayan daukar matakin dokar, maimakon a fatattaki ’yan gwagwarmayar, mayakan kungiyar Boko Haram sai kara karbe iko suke suna korar sojoji daga garuruwa.’Yan gwagwarmayar sun kara zafafa hare-hare inda suke kashe daruruwan mutane da kuma tilasta wa wasu dubbai barin muhallansu. Abin da ake tabka mahawa akai shi ne ko matakin dokar ta-bacin ya kawo wata fa’ida; kodayake, wasu na ganin matakin yana taimaka wa ’yan gwagwarmayar ne kawai. A wani lokaci akwai batun da masu bai wa shugaban kasa shawara da na kusa da shi suke cewa matakin dokar bai kamata ba, wanda kuma ya hada da dakatar da gwamnonin jihohin kasar  da ’yan majalisun jihohin uku ba. Zargin da wannan ya kawo bai zo da mamaki ba kuma ya kara yawan wadanda ke adawa da tsawaita wa’adin dokar.  Amma abin tsoron shi ne an siyasantar da batun.
Dalilin da ya kan sa a kafa dokar ta-baci shi ne saboda a jingine duk wasu hakkoki domin bai wa sojoji ko jami’an tsaro daukar matakan da suka dace. Ana sanya ta ne lokacin wata annoba, ko kuma wani yanayi na rikici da ke barazana ga kasa. Lokacin aiwatar da dokar, ana hana zirga-zirga jama’a a wasu lokuta da kuma killace jama’ar wasu yankuna. Da yake bayyana hujjarsa ta sanya dokar, Shugaba Jonathan ya bayyana cewa hakan zai bai wa sojoji damar ci gaba da yaki ba tare da wani shamaki ba.
Sai dai wannan fatan bai tabbata ba, masu adawa da dokar suna kafa hujja da cewa sharrin dokar ya fi alherinta. Kamar yadda Sanata Mohammed Ali Ndume daga Jihar Barno ya ce dokar ta-bacin tana taimakon ’yan gwagwarmaya ne wadanda suke kaddamar da farmaki lokacin da aka tilasta wa jama’a kasancewa a gidajensu. Shi da wasu masu adawa da dokar sun yi amannar cewa idan da a ce babu dokar, mutane za su fi iya mayar da martani ga hare-haren mayakan Boko Haram da kuma wadata jami’an tsaro da bayanan sirri.
Wannan abin kaicon yana sanya alamar tambaya game da matakan da gwamnati ke dauka kan yaki da ta’addanci, saboda yadda dogaro da dokar ta-baci ya gaza haifar da da mai ido. A lokacin da farmakin ’yan gwagwarmaya yake ci gaba da sha kalaman Allah-wadai, sojoji ba sa saka kaimi, kodayake suna amfani da salon yakin gaba da gaba wajen yaki da zakakuran abokan gaban.
Idan ana so a samu nasara, ya dace sojoji su sauya salon da suke yaki da Boko Haram. A jingine duk wani alfanu da dokar ta-baci take da ita, yamata sojoji su sauya dabara da sake duba yadda ake aikewa da dakaru fagen daga ciki har da kara karfafa masu gwiwa. Har ila yau, shugaban kasa yana da sauran dama da kundin tsarin mulki ya ba shi na amfani da dakarun kasar nan a fagen daga.
Bai kamata sojojin Najeriya da ake jinjina masu wajen samar da zaman lafiya a kasahen duniya, a ce kuma sun gaza yin wata katabus a gida ba. Ya dace Babban Kwamandan Askarawan kasar nan ya cika alkawarin da ya dauka na cewa “zan yi dukkan mai yiwuwa” wajen samun galaba kan masu tada kayar baya.