✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taiye Taiwo zai gina otel din Naira biliyan 3 a Legas

Rahoton da wata jaridar da ake bugawa a Legas mai suna Street Hits ta kalato  a karshen makon jiya ya nuna cewa tsohon dan kwallon…

Rahoton da wata jaridar da ake bugawa a Legas mai suna Street Hits ta kalato  a karshen makon jiya ya nuna cewa tsohon dan kwallon Super Eagles, Taiye Isma’ila Taiwo ya fara shirin gina katafaren otel a Legas da aka kiyasta kudinsa a kan Naira biliyan 3.
Taiye wanda dan asalin Jihar Legas ne da ya fito daga yankin Igando an nuna tun yana  karami yake da burin ganin ya mallaki otel na kashin kansa, don haka a wannan lokaci yake kokarin ganin ya cika wannan buri. Rahoton ya nuna cewa tuni dan kwallon ya mallaki filin da zai fara wannan gini bayan ya samu zanen ginin daga kasar Faransa a lokacin da yake kwallo a can.
Haka kuma rahoton ya nuna baya ga kokarin mallakar otel, Taiye ya sayi wasu filaye a kusa da inda zai gina otel din domin gina wasu rukunan gidaje don ya zuba ’yan haya.
Taiye wanda ya buga wasa ga kungiyoyin kwallon kafa da dama a Nahiyar Turai, ya taba buga wa kungiyar Olympic Marseille ta Faransa da AC Milan da ke Italiya da kueen Park Rangers (kPR) ta Ingila da Dynamo Keib ta Rasha da Burarspor na Turkiyya.  Sannan yanzu haka yana yi wa kulob din Helsingin na Finlan kwallo ne. Yanzu haka Taiye yana da shekara 31 a duniya.
Rahoton ya ce har yanzu mahaifiyar dan kwallon ba ta bar sana’ar sayar da kaya a shagonta da ke Isheri Olofin kusa da wani shatale-tale  a Jihar Legas ba duk da kasancewar danta Taiye ya mallaki dukiya.