“Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, zai kuwa taimake ka, ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.” (Zabura: 55:22).
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai taimako, Mai alheri, Mai jinkai. kaunarSa zuwa gare mu ba ta da iyaka. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan mako inda za mu ga wasu ayoyi daga cikin Littafi Mai tsarki don karfafawa a duk lokutan da muke neman taimako daga wurin Ubangiji.
Gama a rubuce yake, maganar Ubangiji na da iko, abin da ya kamata mu sani a nan shi ne ‘Ban-gaskiya,’ mu zama masu ba da gaskiya ga Ubangiji, Shi kuwa ba zai yashe mu ba, domin ban-gaskiyarmu ga Ubangiji za ta ’yantar da mu. Dalilin da mutane ke fuskantar matsaloli da dama har su ga kamar babu mafaka ko mai taimako shi ne ba su gaskanta da ikon Ubangiji ba, sun fi dogara ga ikon kansu da kuma abin da mutum zai fada musu. Abin da ya kamata mu sani shi ne, Ubangiji Yana da iko, zai kuma taimake mu a duk lokacin da muka fuskanci wata matsala.
Ga wasu ayoyi daga Littafi Mai tsarki da za su taimake mu a duk lokacin da muke neman taimako daga wurin Ubangiji, idan muka yi addu’a da ban- gaskiya ga Ubangiji.
Filibiyawa 4:6-7
“Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsayar da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.
1 Yahaya 5:14-15
“Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roki komai bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu. 15. In kuwa muka san komai muka roka yana sauraronmu, mun tabbata mun samu abin da muka roka a gare shi ke nan.
Matiyu 7:7
“Ku yi ta roko, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta kwankwasawa, za a kuwa bude muku.”
Zabura 46: 1-3
“Allah ne mafakarmu da karfinmu, kullum a shirye yake ya yi taimako a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da duniya za ta girgiza, duwatsu kuma su fada cikin zuzzurfan teku, ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, tuddai kuma su girgiza saboda tangadin tekun.”
Romawa 10:10-13
“Domin da zuci mutum yake gaskatawa ya samu adalcin Allah da baki yake shaidawa ya samu ceto. Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da Shi ba zai kunyata ba.” Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba’al’umme. Ubangijin nan daya Shi ne Ubangijin kowa, Mayalwacin baiwa ne kuma ga dukan masu addu’a a gare Shi. “Duk wanda kuwa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai samu ceto.”
Ibraniyawa 13:5-6
“Kada halinku ya zamana son kudi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kanSa Ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” Saboda haka, ma iya fitowa gaba gadi, mu ce, “Ubangiji Shi ne Mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”
Zabura 107:28-30
“Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu. Ya sa hadari ya yi tsit, igiyoyin ruwa kuma suka yi shiru. Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru, Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya, Wurin da suke so.”
Zabura 124:8, 125:1
“Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi Wanda Ya yi sama da duniya.
Wadanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.”
Zabura 119:169-176
“Bari kukana ya kai gare Ka, ya Ubangiji! Ka ganar da ni kamar yadda Ka alkawarta. Bari addu’ata ta zo gare Ka, Ka cece ni kamar yadda Ka alkawarta. Zan yabe Ka kullum, Domin Ka koya mini ka’idojinKa. Zan rera waka a kan alkawarinKa, Domin umarninKa gaskiya ne. Kullum a shirye Kake domin Ka taimake ni, Saboda ina bin umarninKa. Ina sa zuciya ga cetonKa kwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarKa. Ka rayar da ni don in ya be Ka, Ka sa koyarwarKa su taimake ni! Ina kai da kawowa kamar batacciyar tunkiya, Ka zo Ka neme ni, ni bawanKa, Saboda ban ki kulawa da dokokinKa ba.”
Zabura 146:5-10
“Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, Wanda Ya halicci sama da duniya da teku da duk abin da yake cikinsu. Kullum Yakan cika alkawaranSa. A yanke shari’arsa takan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kubutar da daurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arsa, adalai. Yakan kiyaye baki wadanda suke zaune a kasar. Yakan taimaki gwagware, wato matan da mazansu suka mutu da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamunna! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!”
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ikon ba da gaskiya gare Shi, a cikin sunan Yesu Almasihu, amin.