Allah a cikin ikonSa, tsakanin 10 zuwa 28 ga watan Oktoban da ya gabata na yi bulaguro zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma birnin Alkahira babban birnin kasar Masar a zaman hutu.
A ranar Laraba 10 ga watan na Oktoba muka bar kasar nan ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano da kimanin karfe 2:30pm na rana ta jirgin kasar Masar wato Egypt Air. Bayan tafiyar awa 5 da rabi, wato kimanin karfe 10 na dare na kasar ta Masar sai muka sauka a filin jirgin saman kasar. Daga nan kuma muka samu canjin jirgi na dai Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar ta Masar wanda ya zarce da mu zuwa birnin na Dubai, wanda muka isa da kimanin karfe 5 na asubar can, kasancewar akwai bambancin lokacin awa 3, cur tsakanin kasar nan da kasar ta Dubai.
Bayan mun isa masauki muka kuma rama sallar asuba da ke kanmu, sai aka shiga barcin gajiya kasancewar mun kusa shafe awa 13, muna tafiya. Idan aka yi la’akari da lokacin da muka bar kasar nan da kuma lokacin da muka sauka a kasar ta Dubai, kasancewar kamar yadda na fadi tun farko akwai bambancin awa 3, tsakanin kasar nan da birnin na Dubai wato suke gaba da mu a kan lokaci.
Allah Ya sa ni ban taba zuwa birnin na Dubai ba, kafin wannan lokaci kuma ban taba mayar da hankali ba, walau in yi karatu ko yawan sauraren labarai a kan birnin na Dubai, abin da kawai na sani ko nake gani bai wuce tallace-tallacen birnin ba kamar yadda ake cewa shi ne birni na 4, a duniya da ya fi karbar baki da suke shiga a kullum walau don yin kasuwanci ko kuma yin hutu ko yawon bude idanu.
Alal misali, a kididdigar da aka gudanar a kan masu ziyarar birnin na Dubai a 2013, an gano mutane miliyan 15 ne suka shiga birnin walau ko don yin kasuwanci ko don yawon bude idanu. Waccan kididdiga kuma ta tabbatar da cewa nan da 2020, irin wadancan mutane masu shiga birnin na Dubai za su iya haura miliyan 20.
Ba ko shakka birnin na Dubai ya amsa sunansa na birnin da ya bunkasa a kan cinikayya ta duniya baki daya. Tun daga saukarka a cikin filin jirgin saman za ka yi ta ganin kantuna da shaguna na Kamfanoni da Masana’antu da ’yan kasuwar kasashen duniya daban-daban irin na su Nahiyar Asiya da na Nahiyar Turai da Amurka da makamantansu, da suke tallar irin kayayyakin da suke bukata don sarrafawa, ko suka sarrafa suna neman abokan hulda. Idan ka ce daga saukar ka a filin jirgin sama za ka iya samun abokan huldar da ta kai ka, kuma ka yi ta a nan ka dawo kasar ku ba tare da ka shiga cikin birnin ba to kuwa ba wanda zai ce ka yi karya. Wasu abubuwa da suka burgeni da filin jirgin saman na Dubai, sun hada da irin yadda jirgin kasa mai aiki da lantarki ya ke daukar fasinjojin da suka sauka a filin ya kai su inda ake tantance wadanda suka shigo birnin kuma cikin sauki da girmamawa. Ma’aikatan filin jirgin saman sun yi matukar burgeni kasancewar akasarinsu suna sanye da rigunan da suke tambayar fasinja kamar haka:- “Ko zan iya taimakonka” a cikin harshen turanci, wannan ba karamin ci gaba ba ne.
Yanzu maganar da ake tattalin arzikin birnin na Dubai na daya daga cikin tattalin arzikin kasashen duniya da yake saurin hadaka, ta yadda a shekarar 2014, harkokin sabarta-juyarta na birnin ya samar wa birnin Dalar Amurka biliyan 106.1 ($106.1b). Babban abin da aka ce yake kawo wa birnin na Dubai habakar tattalin arzikin kasa, kasar da a1966, ta fara hako danyen man fetur, kuma yanzu wanda take hakowar bai wuce ganga dubu 50,000 zuwa 70,000 a rana ba, bai wuce irin yadda bayan bayyanar man fetur a kasar Sarki Rashid na wancan lokacin ya dukufa wajen gina birnin a kan batun hanyoyi da gine-gine da tashoshin jiragen sama da na kasa da na ruwa, abubuwan da yanzu birnin na Dubai da su ya dogara kacokan a kan bunkasar tattalin arzikinsa, kasancewar yanzu man fetur bai bayar da abin da ya wuce kashi 2 cikin 100, na kudaden shigar birnin, dadin-dadawa kuma ana hasashen man fetur din zai kare nan da shekaru 20 masu zuwa.
Masu iya magana kan ce hanyar jirgi daban ta mota daban. A Dubai ne na ga irin yadda titin mota yake a kasa, a dama da shi kuma ga na jirgin kasa da tashoshinsa a sama, ta yadda za ka iya gani suna tafiya kafada da kafada. Birnin Dubai kuma ya shahara a gine-gine masu tsananin tsawo a duniya kamar irin ginin su Emirates Towers, da Burikhalifa, da Palm Islands, da otel din nan mafi tsada na Burj Al Arab. Dubai ta kuma shahara da wuraren kashe kwarkwatar ido. Alal misali mun ziyarci lambun Filfilo, lambun da bayan abubuwan da za su kayatar da masu ziyara da aka saba sawa cikin lambuna irin wannan, a duk shuke-shuken lambun ga filfilon nan kana gani yana kai komo. Kar ka yi maganar kasuwanni da manya-manyan kantunan zamani da ake kira Shopping Mall da suka kai 70.
Mai karatu nan zan tsaya da kai a kan birnin na Dubai saboda karancin wuri in dawo da kai kasar Masar ko in ce da kai birnin Alkahira da muka dawo cikin shi a ranar 17 ga watan Oktoba. Abubuwa da dama sun yi matukar burgeni a birnin na Alkahira, kamar irin gine-ginen da suke da su, ta yadda idan ka hau titi hagunka da damanka da wuya ka ga benen da ya dara wani a wajen tsawo, ma’ana dukkan benayensu su kan zama kai daya a wajen tsawo da kuma rashin zoba wani. A birnin Alkahira ne na ga tsofaffin motoci irin su Lada da Fijo GL da Marsandi da dai sauransu wadanda aka yi yayinsu yau sama da shekaru 50, a nan kasar sun bace bat, amma a birnin Alkahira ga su nan suna ta karakaina a manyan titunan birnin, kuma ba wadda za ka ga tana hayaki.
Kasar Masar ta yi suna a kan wuraren yawon bude ido wanda ziyara a wurin ta tabbatar mini da haka in da na ga ’yan yawon bude ido birjik daga kasashe daban-daban wasu suna kokarin su hau dalar wasu kuma suna hawan rakuma ko keken doki ana zagayawa da su, baya ga kaburburan sarakunansu da a wancan lokacin ake kira Fir’auna, har da na Fir’aunan Annabi Musa AS.
Yadda harkokin yawon bude ido suke samar da makudan kudin shiga a Masar, haka kasar ta shahara a kan masu ziyarar ta don neman maganin bature. An ce ma kana iya samun ragin kashi 60 cikin 100, na irin kudaden da za ka kashe wajen neman lafiya idan ka je Masar maimakon wata kasar Turai ko ta Amurka.
Akwai batun kokarin da kasar ta Masar take yi a yanzu ta ganin ta jawo hankalin masu zuba jari ta kasashe daban-daban a kan man fetur da iskar gas da hako ma’adanai da harkokin yawon bude ido da fannin ilmi da ayyukan gona da gine-gine da makamantansu kamar yadda wani littafi da na yi kicibis da shi a wannan tafiyar tawa mai taken “Masar kasa mai damammaki da dama” da aka wallafa a wannan shekarar ya bayyana. Mai karatu rashin fili ya sa dole na tsaya a nan, amma karka tambaye ni yadda na ga wadatuwar ababen more rayuwa irin su wutar lantarki da ruwan sha da tsaro da makamantasu a wadannan wurare da na ziyarta.